
Mambobin majalisar wakilai ta tarayya guda biyu Peter Akpanke da Paul Nnamchi sun koma jam’iyar APC.
Akpanke na wakiltar al’ummomin kananan hukumomin Obanliku/Obudu/Bekwara ta jihar Ribas karkashin jam’iyar PDP.
Nnamchi na wakiltar al’ummomin kananan hukumomin Enugu east/Isi-uzo ta jihar Enugu karkashin jam’iyar LP.
Tajuddeen Abbas kakakin majalisar shi ne ya karanta wasikar sauya jam’iyar ta su a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Akpanke ya alakanta dalilin from ficewarsa daga jam’iyar PDP akan rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyar a yayin da Nnamchi ya ce rikicin shugabancin jam’iyar LP ne ya saka shi daukar matakin ficewa daga jam’iyar.