Yan majalisar wakilai 7 daga Akwa Ibom  6 na jam’iyar PDP da 1 na YPP  sun koma APC

Yan majalisar wakilai ta tarayya 6 ne na jam’iyar PDP da su ka fito daga jihar Akwa Ibom su ka sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC.

Yan majalisar su ne Unyime Idem, dake wakiltar mazabar Ukanafun/Oruk Anam, Esin Etim, dake wakilatar mazabar Mbo/Okobo/Oron/Udung da kuma Ekpo Asuquo wanda yake wakiltar mazabar Etinan/Nsit Ibom/Nsit Ubium.

Sauran sun hada da Uduak Odudoh, mai wakiltar mazabar Ikot Abasi/Mkpat Enin/Eastern da  Okpolupm Etteh, mai wakiltar mazabar Eket/Esit Eket/Ibeno/Onna , da kuma Okon Bassey, dake wakiltar Itu/Ibiono Ibom

Shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Tajuddeen Abbas shi ne ya sanar da sauya shekar ta su a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis inda suka alakanta ficewarsu daga jam’iyar ta PDP da rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyar.

Shima dan majalisar wakilai, Emmanuel Ukpong-Udo na jam’iyar YPP dake wakiltar mazabar Ikono/Ini a jihar ta Akwa Ibom ya koma jam’iyar APC.

Sauya shekar ta su na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya fice daga jam’iyar PDP inda ya koma APC.

More from this stream

Recomended