Yan majalisar wakilai 6 sun koma jam’iyyar APC daga jam’iyun LP da PDP

Yan majalisar wakilai ta tarayya su 5 da su ka fito daga jihar Enugu sun sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa APC.

Yan majalisar da su ka sauya shekar sun hada da Obetta Chidi (Nsukka/Igbo-Eze south federal constituency), Anayo Onwuegbu (Aninri/Awgu/Oji River federal constituency), Dennis Agbo (Igbo-Eze north/Udenu federal constituency), Martins Oke (Igbo Etiti/Uzo Uwani federal constituency), and Nnolim Nnaji (Nkanu east/Nkanu west federal constituency).

Har ila yau  Daniel Asama dake wakiltar mazabar Jos North/Bassa ta jihar Filato ya fice daga jam’iyarsa ta Labour Party inda ya koma jam’iyar APC.

Shugaban majalisar wakilan Tajuddeen Abbas ne ya karanta wasikar sauya shekar yan majalisar a yayin zamanta na ranar Alhamis.

Yan majalisar sun alakanta sauya shekar ta su da rikicin da ya yiwa jam’iyunsu sarkakiya.

Bayan kammala karanta takardar Abbas ya bayyana cewa yan majalisun sun dauki matakin da ya dace da suka koma jam’iyar APC.

Gwamna jihar Enugu, Peter Mbah da kuma shugaban jam’iyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda sun halarci zaman majalisar domin sheda sauya shekar.

More from this stream

Recomended