
Yan majalisar wakilai ta tarayya huɗu daga jihar Ribas sun sauya sheka ya zuwa jam’iyar APC.
Yan majalisar sun haɗa da Umezuruike Manuchim (Port Harcourt I ), wanda ya sauya sheka daga jam’iyar Labour Party ya zuwa APC,
Sauran sun hada da Boniface Emerengwa dake wakiltar mazabar (Ikwerre/Emohua ), Awaji-Inombek Abiante dake wakiltar mazabar (Opobo/Nkoro/Andoni ), da kuma Boma Goodhead (Akuku-Toru/Asari-Toru ) da dukkansu suka sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa APC.
Shugaban majalisar wakilan Tajuddeen Abbas shi ne ya karanta wasikar sauya shekar tasu a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.
Sun bayyana cewa rahoton rikicin cikin gida da jam’iyar PDP ke fama da shi ne ya saka su sauya fita daga jam’iyar.

