Yan majalisar dokokin jihar Zamfara biyu sun fice daga jam’iyar APC

Mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara biyu yan jam’iyar APC sun sanar da ficewa daga jam’iyar  inda suka alakanta hakan da rarrabuwar kai a cikin jam’iyar da kuma zargin rashin adalci daga shugabanninta.

Mai tsawatarwa marasa rinjaye, Hon Nura Dahiru Sabon Birnin Dan Ali dake wakiltar al’ummar Birnin Magaji a zauren majalisar ya sanar da fitarsa daga jam’iyar a wata wasika da ya aikewa da shugaban APC na jihar, Tukur Danfulani.

A cikin wasikar ya bayyana cewa ya dauki matakin ne biyo bayan tattaunawar da ya yi al’ummar da yake wakilta da kuma abokanan tafiyarsa a siyasance.

Har ila yau shima Hon Shamsuddeen Hassan Basko wanda ke wakiltar mazabar Talata Mafara North ya sanar da fitarsa daga jam’iyar ta APC.

A wasikar fita daga jam’iyar Hassan ya ce ya fice daga jam’iyar ne bayan da ya yi waiwaye na tsanaki kan rikicin cikin gida, rabe-rabe da kuma yadda aka mayar da wasu saniyar ware a jam’iyar a matakin Æ™ananan hukumomi da jiha.

More from this stream

Recomended