Yan kunar baƙin wake sun kashe mutane 10 a Madagali

[ad_1]








Aƙalla mutane 10 ne suka mutu biyo bayan wani harin kunar bakin wake biyu a wani wuri dake cike da jama’a a ƙaramar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.

Mazauna garin sun shedawa jaridar Daily Trust cewa mata biyu ne suka tayar da bom din dake jikinsu ta bangaren da ake shiga garin daga Gwoza.

Wani mazaunin garin mai suna, Aura Garga ya fadawa jaridar cewa yan kunar bakin waken sun kai harin da misalin 12 na ranar Asabar inda suka kashe kansu da kuma wasu mutane 10.

Ya ce an kwashe da yawa daga cikin mutanen da suka jikkata ya zuwa asibiti domin samun kulawa.

Jaridar ta gaza jin ta bakin hukumomin soji dake bataliya ta 28 dake Mubi.

Garin Madagali dake da tazarar kilomita 250 daga Yola babban birnin jihar Adamawa ya dade yana fuskantar hare-hare tun bayan da aka samu nasarar kwato garin daga hannun yan Boko Haram a shekarar 2015.




[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...