Cibiyar koyar da shugabanci da zama ‘dan kasa na gari, dake birnin Jos, ita ce ta horar da matasan su dari biyar da saba’in da bakwai (577).
Darakta janar na cibiyar, Mr Jonah Bawa, ya ce sun horar da matasan ne kan yadda zasu yi mu’amula da mutane da sauya tunaninsu, don taimaka wa kasarsu.
Wasu da suka sami horon sun bayyana cewa zasu yi amfani da abin da suka koya don samar da zaman lafiya.
Mai hada shirye-shirye a kungiyar Civilian JTF na jahar Borno, Abba Aji, ya ce gwamnati za ta ci gaba da kula da wadan da suka sadaukar da rayukansu wajen samar da tsaro a jihar.
Wakilin hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mathew Alao, ya yi fatan wadan da suka sami horon za su yi amfani da abin da suka koya wajen sasanta al’umma da inganta tattalin arzikin kasa.