‘Yan gida daya na takarar kujerar sanatan yankin Daura

[ad_1]

Kabir Babba and Ahmad Babba

Hakkin mallakar hoto
Kabir Babba Campaign

Image caption

Ahmad Babba Kaita (dama) da dan uwansa Kabir Babba Kaita

Wasu ‘yan uwa biyu wa da kaninsa za su fafata a zaben neman kujerar sanatan yankin Daura da ke jihar Katsina a Najeriya da za a yi ranar Asabar.

Ahmad Babba Kaita na jam’iyyar APC da dan uwansa Kabir Babba Kaita na jam’iyyar PDP ne ‘yan takarar da suke fafatawa a wannan zaben a mazabar sanata ta arewacin Katsina wanda aka fi sani da yankin Daura.

Kabir wan Ahmad ne domin mahaifinsu daya ne daga garin Kankiya na jihar Katsina.

Ahmad shi ne dan majalisar mai wakiltar mazabar Kankia/Ingawa/Kusada a majalisar wakilan Najeriya.

Shi kuwa Kabir tsohon ma’aikacin hukumar hana fasa kwaurin kayayyaki ne wato kwastam.

‘Yan uwan biyu na neman cike gurbin marigayi Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu a farkon watan Afrilun bana.

Wani abin sha’awa shi ne duk wanda ya yi nasara a zaben na gobe zai kasance wakilin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, domin garin Daura na cikin yankin Katsina ta arewa ne.

BBC ta tambayi wasu ‘yan uwan wadannan ‘yan takarar yadda suka fuskanci wannan lamarin ganin cewa siyasa kan zama wani dalilin samun baraka tsakanin ‘yan uwa.

Hajiya Rabi Babba Kaita da Ali Babba Kaita sun bayyana cewa suna da karfin gwuiwa cewa wannan zaben ba zai kawo rabuwar kawuna a tsakaninsu ba.

Ga yadda hirarsu da Sani Aliyu na BBC ta kasance:

BBC Hausa: Ko yaya dangantaka take tsakanin wadannan ‘yan uwa su biyu a da?

Rabi Babba Kaita: Mu dai mun taso da girmama na gaba da mu. Saboda haka Ahmadu da Baba Kabir su ma haka suka taso.

A yanzu, Baba Ahmadu ya dauki Baba Kabir wanda muka fi sani da Baba Daddy kamar uba kuma yana girmama shi.

Shi kuma Baba Ahmadu, biyayyar nan da aka koya mamu ta sa yana bin Kabir shi sau da kafa. Har gobe idan ka je za ka tadda su tare.

BBC Hausa:Shin siyasa ba ta kawo baraka tsakaninsu ba?

Rabi Babba Kaita: To gaskiya muna ta bibiyar yadda suke tafiyar da al’amarinsu tun da aka fara wannan siyasa. Kuma har yanzu Baba Ahmadu na biyayya ga Baba Daddy, suna zaunawa su yi hira, babu abin da ya sauya tsakaninsu. Kuma mu ma tsakaninmu da su babu abin da ya sauya.

BBC Hausa: To mutanen gari fa, yaya suke kallon wannan lamarin?

Rabi Babba Kaita: Na taba karanta wani abu a Facebook da wani dan Kankia ya rubuta game da wannan siyasar. Ya ce ya lura da yanayin gidan da suka fito.

Sabili da haka ya rubuta cewa ya kamata mutane su yi kamfen dinsu cikin hankali da natsuwa. Saboda duk abin da aka fada wanda ya soki Kabir, to Ahmadu ba zai ji dadi ba, kuma duk abin da aka fada ya soki Ahmadu, shi ma Baba Kabir ba zai ji dadinsa ba.

BBC Hausa: Kina nufin babu wata matsala tsakanin Ahmad Babba da Kabir Babba?

Rabi Babba Kaita: Ana ma yin kamfe kansu na hade, ballantana an gama? Kuma ba yau aka fara irin wannan salon siyasar a nan gidan ba.

BBC Hausa: Ko za kiyi mana karin bayani?

Rabi Babba Kaita: Dama an taba samun ‘yan gidan nan su biyu da suka yi takarar mukamai a jam’iyyun siyasa mabambanta. Da Bishir Babba wanda yayi shugaban karamar hukumar Kankia a jam’iyyar PDP da kuma shi Ahmadu Babba wanda ya tsaya takarar kujerar dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC.

A karshe dukkansu sun sami nasara a kan mukaman da suka nema.

To BBC ta kuma nemi Aliyu Babba Kaita wanda shi ma dan uwan ‘yan takarar ne yadda iyalan gidan Babba Kankia za su tunkari wannan kalubalen a gobe?

BBC Hausa: Wa za ku zaba cikin ‘yan takarar biyu tun da dukkansu ‘yan gida daya ne?

Ali Babba: Ni yaya ne ga Ahmad Babba dan takarar sanata a karkashin jam’iyyar APC. Sannan ni kani ne na shida ko na bakwai ga Kabir Babba, shi ma dan takarar sanata a jam’iyyar PDP.

Kasancewa wadannan ‘yan uwan na takarar kujerar sanata daya daga mazabar arewacin jihar Katsina ya sa mu ‘yan uwansu muka duba lamarin da basira sosai.

Muna da sabanin ra’ayoyi da sabanin tunani kamar kowa, amma wannan bai taba shafar dangantakarmu da juna ba.

BBC Hausa: Ko za ka bayar da wani misalin irin wannan hadin kan?

Akwai wata ‘yar uwarmu da ta yi wa motocin kamfe na wadannan ‘yan takarar kwalliya da sitika. Ta yi wa motar Ahmadu kwalliya da alamar jam’iyyar APC, kana tayi wa motar Kabiru kwalliya da alamar PDP. Duk yawan moocinsu daya, kuma kowa ta ce a je a zabe shi.

BBC Hausa: To idan kun je runfunan zabe, wa za ku zaba a cikinsu?

To mu iyalan gidan mun zauna mun duba yadda za mu tunkari zaben. Kuma a matsayinmu na manyan gidan, mun bayar da shawara cewa gobe kowa ya yi zamansa a gida.

Babu wanda cikinmu zai fita ya yi zabe saboda muna son Baba Kabir kamar yadda muke son Ahmadu Babba.

[ad_2]

More News

Obasanjo ya kai wa Remi Tinubu ziyara

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga, Oluremi Tinubu mai ɗakin shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu . Obasanjo ya ziyarci matar shugaban ƙasar a...

Shehin Musulunci ya nemi masu kuÉ—i da su raba wa talakawa naman Salla

Mataimakin Babban Limamin Masallacin Yobe da Cibiyar Musulunci, Malam Mohammad Ali Goni Kamsulum, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su rika...

Ƴansandan sun yi artabu da ƴanbindiga a Abuja

Jami’an ‘yan sanda daga babban birnin tarayya Abuja sun kashe wani dan bindiga tare da cafke uku a wani samame da suka kai.Ƴan sandan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan...