‘Yan fashi sun yi garkuwa da jirgin dakon mai a Najeriya

'Yan fashin teku a Nigeria sun yi kaurin suna wajen sace matuka jirgin ruwa



‘Yan fashin teku a Najeriya sun yi kaurin suna wajen sace matuka jirgin ruwa

Hukumar kula da sufurin ruwa ta kasa da kasa, ta ce masu fashin teku sun kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a Najeriya inda suka sace matuka jirgin shida.

Hukumar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da ta wuce a kudancin birnin Fakwal na jihar Rivers.

Ta ce an sanar da rundunar sojan ruwa ta Najeriya, kuma an kaddamar da bincike kan batun.

A farkon wannan watan ma, wasu masu fashin teku sun yi yunkurin sace wani jirgin na dakon mai, sai dai rahotanni sun ce sojojin da ke gadin takun kasar sun fatattaki barayin.

‘Yan fashin teku a Najeriya sun yi kaurin suna wajen sace matuka jirgin ruwa da neman kudin fansa, a wasu lokutan kuma sukan sace masu aikin hakar mai da ke yankin Niger Delta.

Ko a watan da ya gabata sai da aka samu makamanciyar wannan hari da ya yi sanadi ran sojan ruwa guda bayan musayar wuta da ‘yan fashin.

Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa abu ne da ya yi kamari a wasu sassan kasar wanda akasari ake farwa baki ‘yan kasashen waje da kuma yawaitar satar danyen mai a gabar tekunta.

Matsalar da ta bazu zuwa gabar tekun Guinea da kasashen da ke kewaye da Najeriyar, kamar su Kamaru da Benin da Gabon.

More from this stream

Recomended