
Wasu yanbindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sunyi awon gaba da wani babban soja,matarsa da kuma yayansu biyu akan hanyar Wukari zuwa Ibbi dake jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa sojan na tafiya ne sanye da kayan gida cikin motarsa tare da iyalan nasa lokacin da yan bindigar suka sace su a kauyen Ibiwa dake karamar hukumar Ibbi ta jihar.
Wasu majiyoyi dake Wukari da Ibbi da suka nemi a boye sunansu sun fadawa wakilin jaridar cewa jami’in na aiki ne da barikin sojoji dake Takum kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Ibbi daga Takum lokacin da yan bindigar suka tsare hanya a kauyen Ibiwa suka kuma dauke shi tare da iyalansa ya zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,DSP David Misal ya ce ya tuntubi baturen yansanda na Ibbi kan faruwar lamarin amma bai bashi amsa kan batun.