Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban jam’iyar APC na wata mazaba

Yan bindiga sun yi garkuwa da Nelson Adepoyigi wani jigo a jam’iyar APC a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo.

Adepoyigi wanda ke shugabantar mazabar Ifon a karamar hukumar anyi garkuwa da shi da maraicen ranar Litinin akan titin Ifon zuwa Owo.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata Olayinka Ayanlade mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce an yi garkuwa da dan siyasar ne lokacin da yake Shiga cikin gonarsa.

Mai magana da yawun rundunar ya ce tuni aka fara aikin bin sawun masu garkuwar a yayin da kuma ya roki mazauna jihar da su taimaka da kowane irin  bayani da zai taimakawa aikin yan sanda wajen kubutar da shi.

” Zan iya tabbatar muku cewa an yi garkuwa da shugaban jam’iyar APC na mazabar Ifon a wajen shiga gonarsa dake kan titin Ifon-Owo,” a cewar  mai magana da yawun rundunar yan sandan.

More from this stream

Recomended