Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 73 a Zamfara

Akalla mutane 73 ne aka bada rahoton anyi garkuwa da su biyo bayan harin da yan bindiga suka kai ƙauyukan Buzugu da Rayau a karamar hukumar Bukuyyum ta jihar Zamfara.

Zagazola Makama dake wallafa bayanan kan sha’anin tsaro ya bayyana cewa an kai farmakin da karfe 02:45 na daren ranar 18 ga watan Oktoba.

A cewarsa yan bindigar masu yawan gaske ɗauke da muggan makamai sun farma ƙauyukan biyu inda suka yi awon gaba da wasu mazauna ciki ya zuwa wani wuri da ba a a sani ba.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ana cigaba da kokarin ganin an kubutar da dukkanin mutanen tare da dawo da zaman lafiya a inda lamarin ya faru.

Har ila yau majiyar ta bayyana cewa jami’an tsaro da kuma yan bijilante dake yankin na cigaba da zafafa bincike a yankin.

Al’ummomi da dama dake jihar Zamfara na cigaba da fuskantar hare-hare daga yan bindiga.

More from this stream

Recomended