Wasu ‘yan bindiga sun kwace kayan abinci da abin sha daga hannun wani mutum da ya tanada don bikin Kirsimeti, yayin da yake kan babur a hanyar kauyen Gidan Abe, Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
Wani basarake a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin, inda ya bayyana cewa abin ya faru ne ranar Asabar da misalin karfe 5:23 na yamma. Mutumin ya dawo daga siyan buhun shinkafa, lemuka, da kayan miya a garin Katari, yana kan hanyarsa ta kauyen Gidan Abe.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar, da ke kan babura, sun tare mutumin sannan suka kwace duk kayan da ke hannunsa. Duk da haka, ba su ji masa rauni ba.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai tabbatar da faruwar lamarin ba.