‘Yan Bindiga Sun Raba Dubban Mutane Da Gidajensu A Zamfara

[ad_1]

Ko baya ga kashe daruruwan rayuka, alamuran ‘yan bindiga dake kai hare hare ya raba dubban jama’a da gidajensu a wasu kauyukan jahar Zamfara,abun da ya haifar da dimbin ‘yan gudun hijira a jihar.

Wata mace da wannan fitina ta shafa, da fadawa MA cewa al’amarin sai a hankali saboda ko zuciyarsu ma an kasheta, an kashe masu rayuwa domin basu san halin da suke ciki ba. Tace a yanzu dai sun tagayyara.

Binciken da Muriyar Amurka ta gudanar ya nuna mutanen da lamarin ya shafa ne ke kafa sansanonin gudun hijira da kansu, ta hanyar fakewa a makarantun boko, da wasu gine-ginen gwamnati, yayinda wasu da dama ke fakewa a gidajen ‘yanuwa da abokan arziki a wasu garuruwan.

Wani ya ya gayawa wakilin Sashen Hausa cewa a garin Mada ba’a rasa ‘yan gudun hijira dubu uku dake fake a makarantar boko, haka kuma a duk cikin garin babu gidan da ba dan gudun hijira.

Makonni biyu da suka gabata gwamnatin tarayyar Nigeria ta tura wata rundunar soji ta musamman domin shawo kan lamarin. Dakarun da aka tura sun hada da sojojin sama da jiragen yaki. Mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Wakala Muhammad, yace matakin ya soma tasiri sosai har ma wasu ‘yan gudun hijiran sun soma komawa garuruwansu.

Wani ganau ya ce sojojin da aka tura wajejen karamar hukumar Zurmi sun fatattaki ‘yan bindiga da dama, sun kashe wasu kuma sun kama wasu. A wajejen Tsafe sojojin na iyakar kokarinsu na murkushe ‘yan ta’addan. Wannan ya taimakawa al’umma suna samu suna komawa gidajensu. Amma har yanzu akwai kalubale a bangaren Maradun da dai wasu wuraren.

Kanar Muhammad Dole, mataimakin jami’in watsa labarai na runduna ta daya dake Kaduna, rundunar da jahar Zamfara ke karkashin kulawarta ya yi tsokaci akan abun dake faruwa. Ya ce shi ciwo rana daya yake shiga, amma magani a hankali yake aiki, wato sannu a hankali ne sojojin zasu shawo kan lamarin.

Kawo yanzu daga jihar Zamfara har zuwa Birnin Gwari sun kai sojoji kowane gari da kauye, musamman wuraren da suka fi yin barna. Bugu da kari sojoji na aiki da mutanen gari cikin tsanaki domin a ciwo kan lamarin. A cewar Kanar Dole masu satar shanu sun ragu.

Akan fargabar cewa wasu ‘yan bindigan na iya kutsawa cikin jihohin dake makwaftaka da Zamfara, Kanar Dole ya ce wannan ma bai taso ba saboda sojojin da suka ajiye a jihohin suna sa ido suna cafke duk wanda suka gani yana da alaka da masu barna

A saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna domin cikakken bayani

[ad_2]

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...