
Wasu yan bindiga sun kai farmaki ofishin yan sanda na garin Zonkwa dake karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna inda suka kashe akalla yan sanda biyu.
Lamarin da ya faru maraicen ranar Juma’a ya jefa mazauna garin cikin fargaba.
Wasu shaidun gani da ido sun fadawa jaridar Daily Trust cewa da isar yan bindigar ofishin yan sandan dake da tazarar mitoci kadan daga Otal din Kamyim dake Kurmin-Bi Zonkwa sun bude wuta inda suka rika harbin kan me uwa da wabi.
An ce sun yi ƙoƙarin kubutar da wasu barayi ne da tun farko aka kama a garin Kachia.
“Sun yi zaton cewa ana tsare ne da wadanda aka kama din a ofishin yan sanda na Zonkwa,” a cewar wata majiya da bata so a ambaci sunanta.
Bayan sun tafka mummunar barnar ne aka gano cewa ba anan ake tsare da mutanen ba.
Har ila yau wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin sai dai ta gaza karin haske kan cikakken abun da ya faru.
Wani fefan bidiyon harin da aka wallafa ya nuna gawar yan sandan kwance cikin jini.