Yan bindiga sun kashe yan bijilante sama da 70 a jihar Plateau

Akalla yan bijilante 70 ne aka kashe a wani harin kwanton bauna da yan bindiga su ka yi musu a garin Bunyun dake karamar hukumar Kanam ta jihar Plateau.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 02:00 na rana.

Aliyu Bappa shugaban yan bijilante na garin Kukawa ya ce an yi kisan ne a wani wuri dake da tazarar kilomita guda daga garin na Kukawa lokacin da yan bindigar suka yi wa yan bijilanten kwanton bauna lokacin da suka nufi maboyarsu dake dajin gwamnati da aka killace da ake kira Madam Forest.

Baffa ya fadawa jaridar Daily Trust cewa da misalin karfe 1:30 na dare ne ya fara ji karar harbi inda mutane suka fara hasashen yan fashi ne suka kawo farmaki garin.

Shugaban ya ce daga baya ya gano cewa harbin na yan bijilante ne da suka fito daga Ruwan Safiyo domin su yaki yan fashin daji a maboyarsu.

“Abun ya bamu mamaki da yan bijilante suka rika dukan mutanen garin mu da basuji basu gani ba. Sun lalata shaguna da sace wayoyin hannu,” ya ce.

“Sun kuma shiga gidajen mutane inda suka kwace wayoyin hannu sama da 150. Sun kwace babura 30 daga mazauna garin inda suka ce za su je dajin fada da yan bindigar,”

Ya kara da cewa yan bijilanten sun zarge su da bawa yan bindigar maboya zargin da suka musalta.

Ya cigaba da cewa daga nan ne suka zarce ya zuwa cikin dajin kuma mintoci 20 bayan shigar su ne suka fara jiwo karar hare-harben bindiga abun da ke nuna cewa ana tafka gumurzu.

Babu jimawa kadan ne suka fara ganin yan bijilanten suna dawowa abun da ke nuna cewa  yan bindigar sun fi karfinsu.

Baffa ya ce bayan sanar da DPO sun binne gawarwarkin mutane sama da 60 a Kukawa kuma akwai yiyuwar samu wasu karin gawarwarkin daya bangaren na dajin.

More from this stream

Recomended