
Rundunar sojan Najeriya ta ce sojoji 17 aka kashe yayin wani farmaki da su kai domin dakile kutsen da yan bindinga su ka yi shirya yi a garin Bangi dake karamar hukumar Mariga ta jihar Niger.
Appolonia Inele mai rikon mukamin daraktan yada labarai na rundunar a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba ya ce an kai harin ne a ranar Litinin.
Ta ce sojojin sun gwabza da yan bindigar da yawansu ya kai 300 lokacin da suke wucewa ta dajin Kwanar Dutse akan hanyarsu ta zuwa Kwatankoro inda aka yi mummunar musayar wuta.
Ta ce an kai farmakin ne tare da hadin gwiwar sojan sama bisa dogaro da gamsassun bayanan sirrin da aka samu.
Ta kara da cewa sojojin sun dauki tsawon sama da sa’o’i 3 suna musayar wuta da yan bindigar kafin sojan sama su yi musu liguden wuta akan hanyarsu ta tserewa.
“Batagarin sun yi kokarin tafiya zuwa Dajin Kwatankoro da daddare inda aka rawaito za su tsara kai hare-haren garuruwan dake kusa da kuma samun mafaka daga zafafafan hare-hare da ake kai musu a jihar Zamfara,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa sojoji 10 ne suka samu raunuka daban-daban.
Ta kara da cewa ba a iya tabbatar da yan bindiga nawa suke mutu ba a gumurzu da aka yi amma anga alamar jini da dama a hanyar da da su ka bi su ka tsere.