‘Yan bindiga sun kashe mutum 20 a Burkina Faso

Burkina Faso

Mutane 20 maharan suka kashe a harin kauyen Bani

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari da tsakar dare a arewa maso gabashin Burkina Faso, kuma farar hula 20 ne suka mutu.

‘Yan bindigar da sun kai harin a daren Asabar akan babura dauke da muggan makamai, sun afkawa kauyen Bani, da ke arewacin birnin Ouagadougou, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.

Wannan hari na zuwa ne mako guda da ‘yan bindiga suka kai hari kasuwar Silgadji da ke yankin, tare da hallaka mutane 39.

Yankin Sahel dai na fama da hare-harenb ‘yan bindiga da mayakan jihadi a dan tsakanin nan.

Bayanan harin ranar Asabar na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Faransa ta sanar da tura karin dakaru 600 yankin Sahel, wanda hakan ya kai adadin sojojin kasar a yankin 5,000 dan tabbatar da zaman lafiya da yakar mayakan jihadi.

A shekarar da ta gabata yankin ya fuskanci kashe-kashen mutane sama da 4,000 daga mayakan jihadi, wanda aka dade ba a ga irinsa ba tun shekarar 2011.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...