Yan bindiga sun kashe mutane uku a Plateau

Mutane uku aka kashe a wani hari da wasu yan bindiga suka kai ƙauyukan Suwa da Ding’ak dake karkashin masarautar Mushere a karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.

Mutanen  da aka kashe sun hada da Gideon Katings  fasto a cocin COCIN dake Suwa da Sunday Ringkang da kuma Meshach Bukata.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kefas Mallai shugaban kwamitin dake sanya idanu kan zaman lafiya na al’ummar yankin ya ce an kai harin ne tsakanin karfe 1 zuwa 2 na ranar Juma’a.

Jaridar Punch ta ruwaito Mallai na cewa wani mai suna, Michael Kamshak da wasu mutane da dama sun samu raunuka kuma suna samun kulawa a karamin asibiti dake Bokkos.

Mallai ya kara da cewa daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu a sakamakon harin.

More from this stream

Recomended