’Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Tara A Ɗan Dume Duk Da Cewa An Yi Sulhu

Ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a garuruwan Kauran Fawa da Unguwar Jika, da wasu yankuna a ƙaramar hukumar Ɗan Dume ta Jihar Katsina, bayan wani hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai, inda aka kashe mutum tara tare da jikkata wasu 13.

Harin ya faru ne cikin daren Alhamis, duk da sulhun da masu ruwa da tsaki a yankin suka jagoranta da ’yan bindigar, domin dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Hukumomin yankin sun ce sun halarci jana’izar mutum biyar, yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakai na tabbatar da tsaro a yankin.

Wani mazaunin ɗaya daga cikin garuruwan da abin ya shafa, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa ’yan bindigar sun shiga garin ne a ƙafa suna harbe-harbe.

“Mutum tara ne suka mutu sakamakon harbin da yanbindigar suka yi, sannan 13 ne suka samu raunuka inda muka kai su asibiti domin samun kulawa. Sun ɗauki mutum aƙalla goma amma sai suka yi ta sakin mutanen sakamakon artabu. Mutum ɗaya ne ya rage a hannun su,” in ji shi.

Shugaban ƙaramar hukumar Ɗan Dume, Bishir Hadi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tare da shi aka yi jana’izar mutanen da aka kashe.

“Mun yi sulhu kuma mun samu nasara, tsawon wata biyar ba a kawo hari ba sai yanzu. Kafin yanzu babu ranar da ba a kawo mana hari,” in ji Bishir.

Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta daɗe tana fama da hare-haren ’yan bindiga, duk da sulhun da gwamnatin jihar ta yi da su tare da sakin wasu da aka kama, matakin da hukumomi ke cewa an ɗauke shi ne bisa yarjejeniyar wasu al’ummomi domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

More from this stream

Recomended