‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Takwas, Sun Sace Wasu a Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a safiyar Lahadi a kauyen Wake da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane akalla takwas tare da jikkata kimanin 20.

Bayan haka, maharan sun yi awon gaba da wasu mazauna yankin zuwa wani wuri da ba a sani ba. Rahotanni sun nuna cewa yawancin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali, kuma an kwashe su zuwa asibiti domin samun magani.

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun shiga garin da tarin yawansu, suka kashe, suka raunata, sannan suka yi garkuwa da jama’a ba tare da wata turjiya daga jami’an tsaro ba.

Ya ce, “mutanen da aka kashe an riga an binne su, yayin da wadanda suka jikkata ke karɓar magani, amma har yanzu ba mu san inda aka kai wadanda aka sace ba.”

Mazaunin ya kuma roƙi gwamnatim tarayya da ta jihar Kaduna da su gaggauta tura jami’an tsaro a yankin don dakile hare-haren da ake ta fama da su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai samu damar yin karin bayani kan lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi.

More from this stream

Recomended