Yan bindiga sun kashe mutane 4 a jihar Neja

Mutanen da basu gaza huɗu ba ne aka kashe bayan da wasu yan bindiga su ka kai farmaki kauyen Damala dake gundumar Woku a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Harin na zuwa ne ko mako guda ba ayi ba  da kashe mutane 42 a wasu farmaki da aka kai kan wasu garuruwa dake karamar hukumar Borgu da Agwara a jihar ta Neja.

Jaridar The Cable ta gano cewa harin na baya bayan nan an kai shi ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Juma’a lokacin da mutane suka shiga gidajensu.

Wasiu Abiodun mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Neja ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce mutane akalla huɗu aka kashe.

” A ranar 10 ga watan Janairu da farkon daren ranar wani rahoto da aka samu ya nuna cewa wasu da ake zargin yan fashin daji ne sun kai farmaki kauyen Damala ta gundumar Woko a karamar hukumar Borgu inda suka sace shanu aka kuma kashe kusan mutane huɗu a cikin kauyen,” a cewar Abiodun a zantawar da ya yi da jaridar The Cable.

Mai magana da yawun rundunar ya ce an kuma kone wasu shaguna a lokacin.

More from this stream

Recomended