
Akalla mutane 12 aka kashe a yayin da aka yi awon gaba da wasu da ba a san yawansu ba a wasu jerin hare-hare na ramuwar gayya da wasu yan bindiga suka kai kan kauyuka da dama a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
A ranar 03 ga watan Mayu ne rundunar sojan Najeriya Birged ta 1 ta sanar da kisan wasu jagororin yan bindiga a jihar Zamfara tare da gano wasu makamai.
Farmakin da rundunar ta kai a kananan hukumomin Talata Mafara da Kauran Namoda an bayyana shi a matsayin kokarin da dakarun soja keyi na kakkabe yan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
Arangamar da aka yi ta jawo mutuwar yan fashin daji da dama ciki har da wasu manyansu da suka hada da Auta Jijji, Dankali, Sagidi, Kachallah Rijaji, da kuma Kachallah Suza.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi an kai harin na ramuwar gayya ne a ranar 05 ga watan Mayu da karfe 01:30 na rana.
Ya bayyana cewa harin martani na farmakin da sojoji suka kai kan sansanin yan fashin daji dake dake dajin Dankurmi.
A cewar rahotanni yan fashin dajin sun kai farmaki garuruwa 7 dake gundumar Dankurmi da suka hada da Zamfarawa, Kurukuru, Dogon Daji, Dan Hayin Zamfarawa, Tungar Zabo, Burmukai, da Dambawa inda suka kashe mutane 12 tare dauke wasu ya zuwa wani wuri da ba a sani ba.