Yan bindiga sun kashe matafiya 2, su ka yi  garkuwa da 3 a Kwara

Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu uku a kauyen Gammu dake kusa da garin Babanla a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.

An kai wa mutanen hari ne lokacin da tayar motar su ta yi faci a kusa da kauyen akan hanyar su ta dawowa Babanla daga Lagos.

A dai-dai lokacin da su ke kokarin gyaran tayar motar ne sai wasu yan bindiga suka far musu inda su ka bude musu wuta.

Wadanda suka mutu a harin sun hada da Alhaji Abdulrazak Ewenla dan asalin kauyen Ajile da kuma Jimoh Audu daga kauyen Ganmu.

Biyo bayan harin wata tawagar jami’an tsaro da suka hada da sojoji, yan sanda da kuma yan bijilante sun isa wurin domin kwantar da hankali tare da bin sawun yan bindigar.

Rundunar yan sandan jihar a wata sanarwa da ta fitar  ranar Alhamis ta bakin mai magana yawunta, SP Adetun Ejire-Adeyemi ta tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai kuma ta ƙaryata bidiyon da ake yadawa cewa mazauna kauyen sun tsere daga garin tamkar kauyen ya zamo kufai.

More from this stream

Recomended