
Yan bindiga sun kashe wani dan sanda tare da wasu mutane biyu a wani harin kwanton bauna da suka kai wa jami’an tsaron dake aikin sintiri a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro kan yankin tafkin Chadi ya ce an kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar jami’in dan sandan da kuma mutanen biyu a ranar Lahadi akan titin kauyen Ajimaka zuwa garin Rukuni
Makama ya ce tawagar jami’an tsaro na aiki ne da rundunar Operation Restore Peace karkashin jagorancin Insifecta Jampi Mbursa an yi musu kwanton bauna lokacin da suke aikin sintiri da suka saba tare da yan bijilante na garin.
Ya ce maharan sun kashe Mbursa tare da wasu fararen hula biyu Julius Igbogh da Raphael Julius dukkansu mazauna kauyen Ajimaka.
Ya kara da cewa maharan sun yi awon gaba da bindigar jami’in tsaron kirar AK-47 dake cike da harsashi guda 30.
An kai gawarwakin mutanen asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu kafin daga bisani a ajiye su a dakin ajiye gawarwaki.

