
Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun harbe wani insifectan dan sanda da kuma wani dan bijilante a garin Zhibi dake makotaka da garin Dei-Dei a karamar hukumar Tafa ta jihar Niger.
Jami’in dan sandan, Joshua Haruna na aiki ne da rundunar yan sandan kwantar da tarzoma ta 45 dake Dei-Dei a yayin da marigayi, Joshua Garba dan bijilante ke aiki da kungiyar yan bijilante dake garin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a baya dan sandan na zaune a cikin barikin yan sanda dake Dei-Dei kafin ya dawo garin da iyalansa bayan da ya samu ya gina gida shekaru biyu da suka wuce.
“Yana taimakawa wajen shiga aikin sintiri da daddare a duk lokacin da yake a gari inda yake jagorantar yan bijilanten garin,” a cewar wata majiya dake garin.
” A baya an taba kai farmaki gidansa inda ya fatattaki maharan amma bayan kwana biyu sai suka bar masa wasikar gargadi da ya dena shiga aikin sintirin dare tare da barazanar cewa za su dawo a kowane lokaci, “
Yan bindigar sun isa garin ne a wata mota kirar Sienna da karfe 09:00 na dare suka kuma tsaya a wani wuri da ba mutane sosai hakan ya ja hankalin dan bijilante inda suka isa tare da dan sandan domin su ji dalilin da ya kawo su nan take kuwa suka bude musu wuta.
Dan sandan ya mutu nan take a wurin a yayin da dan bijilanten ya mutu a asibitin Kubwa dake Abuja