Yan bindiga sun kai farmaki tare da dauke wani mutum  wani rukunin gidaje a Abuja

Yan bindiga sun kai farmaki rukunin gidaje na Grow Homes Estate dake Kubwa a Abuja inda suka yi awon gaba da mutane biyu.

Lamarin ya faru ne a tsakanin karfe 12 zuwa 1:30 na daren ranar Litinin.

Da take tabbatar da faruwar lamarin mai magana da rundunar yan sandan birnin, Josephine Aneneh ta ce da karfe 01:00 yan sanda dake bakin kofar shiga rukunin gidajen suka samu kiran kai daukin gaggawa kan harin yan bindiga.

Adeh ta ce jami’an yan sanda sun gaggauta isa wurin.

Da isar su sun gano cewa yan bindigar sun shiga rukunin gidajen ne ta katangar baya da take waye rukunin gidajen inda suka dauke mutanen da karfin tuwo.

“Yan sandan da suka isa wurin sun yi mustard wuta da maharan na tsawon kusan mintuna 30 inda suka ceto  daya daga cikin mutanen inda suka ceto daya daga cikin mutanen mai suna Chinyere Joe abin yakai ci sun tsere da daya mutumin,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa tuni sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro suka kaddamar da farautar maharan.

More from this stream

Recomended