
Yan bindiga sun kashe wani lauya da kuma mutumin da yake karewa lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga kotu ranar Alhamis a jihar Anambra.
Tochukwu Ikenga mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Anambra wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ya ce an harbe mutanen biyu har lahira da misalin karfe 11:30 na safe a kauyen Egbebelu dake garin Nanka a karamar hukumar Orumba North ta jihar.
Ya ce tunda farko lauyan ya samu nasarar karbo belin wani da ake zargi da kisan kai a babbar kotu ta II dake garin Ekwulobia kafin maharan su tare musu hanya.
Sanarwar ta ce kwamishinan yan sandan jihar, Ikioye Orutugu ya jagoranci tawagar jami’an tsaro ya zuwa wurin da aka aikata laifin.
Ya kara da cewa wani mutum guda ya jikkata sosai a lokacin harin kuma tuni aka Kai shi asibiti.