Akalla mutane 34 ne aka kashe bayan da wasu barayi dake dauke da bindigogi suka kai hari wasu kauyuka uku dake karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara ranar Juma’a.
Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Gidan Wawo-Katuru,Tungar Kaho-Galadi da kuma Kyalidu Katuru.
Wata majiya ta fadawa jaridar The Cable cewa maharan da suka zo akan babura sun cinnawa gidaje da dama wuta ya yin da suka harbe duk wanda suka yi arba da shi.
Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar, Muhammad Shehu ya tabbatar da hare-haren inda ya ce tuni komai ya cigaba da tafiya yadda suke a wuraren da lamarin yafaru.
Shehu ya ce kwamishinan ƴansandan jihar,Usman Nagogo tare da mataimakin gwamnan jihar sun jagoranci wata tawaga da ta halarci jana’izar mutanen da suka mutu.