Wasu ‘yan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya sun kama tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano, Mu’azu Magaji.
Lauyansa da kuma iyalansa sun tabbatar wa BBC cewa an kama tsohon Kwamishinan ne ranar Alhamis da daddare lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa masaukinsa bayan ya gama harkokinsa na ranar.
Lauyansa, Barrister Garzali Datti Ahmad, ya shaida wa BBC Hausa cewa suna zargin gwamnatin Kano ce ta tura ‘yan sanda Abuja suka kama shi.
Mu’azu Magaji, wanda ake yi wa lakabi da Ɗan Sarauniya, ya dade yana sukar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje tun ma kafin a sauke shi daga kan mukaminsa.

Yadda aka kama shi
Barrister Garzali ya ce ‘yan sandan sun kama Mu’azu Magaji ne bayan sun bi motarsa a guje suka suka jefa shi cikin kwatami.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
A cewarsa, daga nan ne tsohon Kwamishinan ya tsaya inda su kuma suka cakume shi suka jefa shi a cikin motarsu suka yi gaba.
Ya kara da cewa siyasa ce ya “sanya aka turo ‘yan sanda daga jihar Kano har Abuja domin su kama shi tun da ka ga ba shi da wani tarihi na aikata laifi.”
Barrister Garzali ya ce za su bibiyi lamarin da zummar daukar matakin shari’a, yana mai cewa “ba za mu bari wani mutum da yake ganin ya isa ba ya karya doka kuma a kyale shi.”
Dama dai tsohon Kwamishinan ya yi fice wajen caccakar Gwamna Ganduje, musamman bayan da tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokoki sun balle daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar suka kafa nasu tsagin da suka kira G-7.
Kazalika Mu’azu Magaji ya sha wallafa sakonni a shafinsa na Facebook inda yake cacakar gwamnatin Ganduje, wadda ya bayyana a matsayin wacce ba ta da alkibla.
A baya dai, Gwamna Ganduje, ya dakatar da tsohon Kwamishinan daga aiki bayan ya wallafa wasu sakonni da ake gani na murna ne da mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya sakamakon cutar korona.
Sai dai Mu’azu Magaji ya sha cewa ba murna ya yi da mutuwar Malam Kyari ba.