Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Rivers ta kama wani mutum mai suna Abi Baragon, mai shekaru 46, bisa zargin dukan wata budurwa tare da jikkata ta bayan ta ki amincewa da tayin aurensa a birnin Port Harcourt.
Rahotanni sun bayyana cewa Baragon, wanda ya riga yana da yara hudu, ya kai harin ne a yankin Nkpolu-Oroworukwo da ke Mile 3, Port Harcourt.
An cafke shi ne bayan wani faifan bidiyo ya yadu a kafafen sada zumunta, inda aka ga budurwar tana neman taimako bayan da mutumin ya yi mata duka sannan ya tsere daga wurin.
Mai magana da yawun rundunar, SP Grace Iringe-Koko, ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a a Port Harcourt. Ta ce jami’an sashin kare hakkin dan Adam na rundunar sun kama wanda ake zargin ta hanyar bin sahun bayanai da kuma amfani da fasahar ganowa.
Yadda Wani Mutumi Ya Lakaɗa Wa Budurwasa Duka Bayan Ta Ki Amincewa Ta Aure Shi
