Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta ce ta ƙaddamar da wani gagarumin atisaye domin tunkarar matsalolin tsaron da ke damun ƙasar.
Rundunar sojin ta kira ƙaddamar da atisayen ne da ta kira Operations “Golden Dawn” da “Still Water” da “Enduring Peace” a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Janar Faruk Yahaya cikin sanarwar da rundunar sojin ta fitar ranar Talata ya ce an ƙaddamar da atisayen ne domin magance ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane da fashi da makami da rikicin makiyaya da dukkanin ayyukan ɓarna a Najeriya.
Kuma sabon yunƙurin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar tashin hankali a yankin ƙabilar Igbo da ke kudu maso gabashi da matsalolin ƴan fashi da makami da hare-haren Boko Haram da Iswap a shiyyoyin kasar.
Manjo Shu’aib Umar, wanda ya yi magana a madadin babban daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan ƙasa, Birgediya janar Onyema Nwachukwu, ya shaida wa BBC cewa za a gudanar da atisayen sojin ne lokaci guda a faɗin ƙasar.
Yankunan da za a yi atisayen
Manjo Shu’aib Umar ya ce bayan atisayen Enugu, za a kuma yi atisayen a runduna ta biyu a Ibadan da runduna ta shida da ke Fatakwal da runduna ta 81 da ke Legas, da kuma yankunan ajiye bayanan sojojin kasa da runduna ta musamman ta 401 da kuma birget ta fadar shugaban ƙasa.
Kuma atisayen ya ƙunshi rundunonin da za su yi yaƙi da matsalolin tsaro a yankunan Najeriya guda huɗu.
Rundunar ta ce rundunar ‘Operarion Still Water’ zai magance matsalolin tsaro lokacin bukukuwan kirsimeti a Lagos da Ogun.
Sauran rundunonin kuma ‘Enduring Peace’ da ‘Golden Dawn’ zu su tabbatar da tsaro a kudu maso kudu da kuma arewa maso yammaci.
Rundunar ta ce shirin na tsawon wata ɗaya ne da aka saba gudanarwa a shekaru kamar rawar macijiya da rundunar murmushin kada wanda aka sauya a yanzu.
Kuma za a ci gaba da atisayen wanda aka ƙaddamar a ranar Litinin har zuwa 24 ga watan Disamba, domin magance matsalolin tsaro.
Manufar atisayen
Babban hafsan sojin Najeriya Janar Faruk Yahaya ya ce manufar yin atisayen shi ne tabbatar da dawo da doka da oda a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro da kuma samar da yanayin da al’ummar za su ci gaba da tafiyar da harakokin ba tare da wata fargaba ba.
Janar Faruk Yahaya ya ce rundunar za ta yi aiki da haɗin gwiwar ƴan sanda da dukkanin hukumomin tsaro na Najeriya domin magance dukkanin matsalolin tsaron ƙasar.
Ya kuma ce wannan atisayen za a yi shi ne bisa doka kamar yadda kundin tsarin mulki za a tabbatar da kare rayukwa da dukiyoyin al’umma ba tare da an taozarta ko an ci mutuncin wani ba.
Rundunar ta yi kira ga al’ummar kasar kada su firgita musamman idan sun ga zirga-zirgar makamai da kayan yaƙi a lokacin atisayen.
Sojojin kuma sun nemi haɗin kan al’ummar Najeriya wajen taimakawa da bayanai domin magance miyagun ayyukan matsalolin tsaron ƙasar.
A makon da ya gabata ne rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da farmakin yaƙi da ƴan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya, wanda ya kai ga katse hanyoyin sadarwa a yankin
Sojojin kuma na ci gaba da yaƙi da mayakan Boko Haram da Iswap a arewa maso gabashin Najeriya.
Yawan rundunonin soji
Najeriya ta shafe shekaru tana fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashi da matsalar ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane a arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya.
Akwai kuma matsalar masu fafutikar ɓallewa daga ƙasar a yankin kudu maso kudu da kudu maso yammaci.
Girman matsalolin tsaron a sassan ƙasar ya raba rundunar sojin Najeriya, inda ta kafa rundunoni a yankunan ƙasar domin kawo ƙarshen matsalolin.
- Operation TURA TAKAIBANGO
- Operation LAFIYA DOLE
- Operation Hail Storm
- Operations SAFE HAVEN
- Operation WHIRL STROKE
- Operation THUNDER STRIKE
- Operation Hadarin Daji
- Operation SAHEL SANITY
- Operation DELTA SAFE
Dubban mutane aka kashe tare da raba miliyoya da gidajensu a hare-haren Boko Haram da ƴan bindiga masu satar mutane a arewacin Najeriya.
Tun kafin hawan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ɗaya daga cikin manyan alƙawura uku da ya yi shi ne na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa musamman a arewa maso gabashin ƙasar.
Ko da yake gwamnatin Buhari ta APC na cewa tana iya ƙoƙarinta na kawo ƙarshen matsalolin tsaron musamman a yankin arewacin ƙasar.