Yadda rashin sanin asali ke taba rayuwar yara

[ad_1]

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda rashin sanin asali ke taba rayuwar yara

asalina

Image caption

Sau da yawa, wadanda suka taso a cikin irin wannan yanayi na rashin sanin uba ko ma uwa da uba kan fuskanci tsangwama da kyara daga al’umma

Gidan marayu nan ne wajen da ke zamewa yaran da aka tsinta, ko wadanda iyayensu suka mutu sanadiyar hatsari kuma aka kasa gane danginsu gidan zama na dindindin.

Zubar da yaran da aka haifa ba bisa aure ba, ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a Najeriya, musamman a arewacin kasar.

Hakan na faruwa ne sakamakon irin abun kunyar da ke tattare da haifar yara ba ta hanyar aure ba, inda iyayen ke ganin gara su jefar a kwata, ko kududdufi ko bola ko su ajiye a wajen wucewar mutane maimakon sun rike a wajensu.

Wasu ko ba a jefar da su ba, to su kan taso cikin rayuwa ta kunci, don yadda ake nuna musu kyama kan nasabarsu, wato haihuwarsu ba tare da aure ba.

Kamar dai yadda wata mata da ta bukaci na sakaya sunanta ta shaida min, “Babu abun da ke tunzura zuciyata ya sa ni bakin ciki da kuka irin idan na tuna cewa ban san waye mahaifina ba.”

Duk da cewa shekarunta a yanzu 35, wannan mata ta ce ba za ta taba daina kuka ba a rayuwarta in har ba ta gano waye mahaifinta ba.

“Duk da cewa na san mahaifiyata, amma rashin sanin mahaifina da sanin hanyar da na fito ba karamin saka ni kuka take ba duk da tarin shekarun, kuma abun bacin ran shi ne yadda mahaifiyar tawa take kin amsa tambaya ta son sanin mahaifina,” in ji ta.

Image caption

Mace

Yawanci idan aka tsinci irin wadannan yara, waje na farko da ake fara kai su misali a jihar Kano, shi ne ofishin hukumar Hisbah, ko wajen masu unguwanni ko dagatai. Su kuma daga nan sai su mika su ga Sashen Walwala da Jin Dadi na jiha wato Social Welfare.

Daktra Zahra’u Umar, ita ce mataimakiyar shugaban hukumar Hisba a jihar Kano, ta kuma shaida min cewa: “A kalla mu kan samu jariri daya a wata, wani lokaci kuma idan abun ya birkito ma sai mu samu har zuwa jarirai hudu a wata.”

Ta ce mafi munin irin wannan lamari shi ne yadda mafi yawan yaran da ake tsintowa jarirai ne, “Kuma an fi jefar da su a kwata ko a bola ko kududdufi, amma cikin ikon Allah a hakan a mafi yawancin lokuta da ransu ake kawo mana su.”

Alhaji Mai-Fada Ali, shi ne mai unguwar Gama B da ke Brigade a Kano, kuma majalisarsa na daga cikin wuraren da “in dai ana neman yaran da suka bata, aka zo nan ba a samu ba, to yawanci sai a fidda tsammani”, kamar yadda ya shaida wa BBC.

“Ana kawo mana yara ‘yan tsintuwa daga jarirai har zuwa wadanda suka dan tasa. Wasu ma za ku ga tamkar dama iyayen sun shirya tsaf ne kafin su kawo su, don har da kayansu ake hadawa a ajiye su.”

“Duk da cewa ba ma ajiye yawan yaran da ake kawowa, amma a kalla a wata wani lokacin sai a kawo mana yara kamar 40. Wani sa’in kuma sai a kwana biyu ma ba a kawo ba,” in ji Mai Unguwa Mai-Fada.

Ina ake kai su?

Dukkan bayanan da hukumar Hisba da Mai-Unguwa suka yi sun nuna cewa a kan kai yaran ne ga hukuma, wato Sashen Walwala da Jin Dadi da ke karkashin ma’aikatar mata ta jiha don daukar bayanansu, daga can kuma sai a kai su Gidan Marayu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rashin sanin nasabar mutum babban tashin hankali ce kamar yadda mafi yawan wadanda ke cikin irin wannan hali suka shaida wa BBC

Amma kafin nan sai an kai su asibiti don duba halin lafiyarsu sun yi kamar mako biyar a can.

“Wani lokaci kuma sai na tafi da su gidana sun kwana biyu ma kafin a kammala cike takardun daukar bayanansu,’ in ji Malama Zahara’u.

Wasu mutanen daga cikin al’umma kan bukaci a ba su irin wadannan yara don su dauki nauyin kula da su tare da zame musu iyaye.

Mai Unguwa Mai-Fada ya ce: “Akwai yarinyar da aka kawo mana nan sai wata mata ta bukaci a ba ta, amma bayan an kwana biyu sai ake ta yi mata gori kan cewa ta dauko ‘yar da ba ta sunna ba, sai ta dawo da ita.

“Sai mai dakina ta ce ba sai mun mayarwa hukuma an kai gidan marayu ba, mu rike ta kawai.”

A yanzu dai Mai Unguwa yana rike da irin wadannan yara har biyu.

Me ke faruwa a Gidan Marayun?

Gidan Marayu na Nassarawa na daya daga cikin gidajen da ake kai wadannan yara don rayuwa ta dindindin, har zuwa lokacin da za su yi aure ko kuma idan aka yi sa’a iyayensu suka bullo don nemansu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a iya cewa yaran da ke gidan marayu na Nasarawa sun yi sa’a da samun ingantaccen wajen zama idan aka kwatanta da wasu a nahiyar Afirka, kamar wannan hoton da ke nuna wani gidan marayu a Nairobi na kasar Kenya

A ziyarar da tawagar BBC ta kai, ta fahimci cewa gida ne mai girman gaske da yake da bangarori daban-daban da dakuna da makarantar Islamiyya da filin wasa da dakunan girki da dakunan zama don hutawa masu kayan kallo da dai sauran su.

Hajiya Lauriya Sagir Garba ta ce “Yanzu ‘ya’yanmu guda 65 a gidan nan, maza 44 sai mata 21. Shekarunsu sun fara daga wata biyu zuwa shekara 31.

“Yaran suna zuwa makarantun boko a cikin gari wadanda suka hada da na gwamnati da na kudi, sannan suna islamiyya a nan cikin gida.

“Akwai masu kula da su dare da rana, kuma muna mu’amala da su irin ta ‘ya’ya da iyaye don ganin mun debe musu kewa,” in ji Hajiya Lauriya.

Cikin yaran da muka tattauna da su a wannan gida, sun shida mana cewa suna matukar jin dadin rayuwarsu don ana wadata su da duk abun da yara ke bukata.

“Muna cin abinci sau uku, wani lokaci ma sau hudu a rana. Muna wanka sau biyu, sannan muna da suturu da dama, don gaskiya mutane na waje ma na iya kokarinsu wajen kawo mana ziyara da wadata mu da kayan bukatu,” in ji wata matashiya mai shekara 18 da muka boye sunanta.

Kewa

Sai dai duk da irin wannan daula da yaran ke ciki, hakan bai hana masu wayo daga cikinsu kewar mahaifansu da ba su ma san su waye ba.

Hajiya Lauriya ta ce duk kokarin da suke na ganin sun cike wa yaran nan gurbin iyaye da suka rasa, “to wani lokacin sai an ga alamar damuwa a tare da masu wayo daga cikinsu, kuma damuwar ba ta komai ba ce sai ta rashin sanin asalinsu.”

Habu (Ba sunansa na gaskiya ba) matashi ne mai shekara 18 da shi ma yake gidan, ya kuma shaida min cewa ba shi da wani buri da ya wuce Allah ya sa yana da rabon ganin iyayensa ko wani jininsa a duniya.

“Duk da cewa ba abun da nema na rasa a gidan nan, amma duk dare idan na kwanta sai na yi ta fatan ina ma wata rana na hadu da mahaifana ko wasu dangina. Ban dai fidda tsammani ba,’ in ji Habu, kamar dai yadda da dama daga cikin yaran ma suka shaida min irin wannan magana.

Aure

A gidan marayu Hajiya Lauriya ta shaida min yadda suke aurar da ‘ya’yan nasu, bayan sun kammala karatu.

Ko a loakcin da muka kai ziyara ma mun iske ana shirye-shiryen bikin daya daga cikin yaran maza, don har mun ga lefensa.

“Duk lokacin da suka kai aure in dai sun samu masu son su to biki muke shirya musu na bajinta a nan gidan. Sannan mu kan kai wasu hidimomin kamar Kamu ko liyafa gidajen manyan jami’an gwamnati ko gidajenmu tamkar yadda ake kai biki sauran ‘ya’ya gidajen ‘yan uwansu,” a cewar Hajiya Lauriya.

Sai dai a wasu lokutan samun abokan rayuwa na iya yi wa wadannan yaran wahala, don ganin yadda al’umma take jinjina batun asali a wajen neman aure.

Na hadu da wata matashiya da akai wa aure a gidan amma auren ya mutu bayan shekara daya, kuma ta ce min har da gorin da ake mata a dangin mijin cikin sanadin mutuwar auren.

“A kan yi min gori wasu lokutan cewa ba ni da iyaye ko asali, abun dai ba dadi,” in ji ta.

Image caption

Sau da yawa, wadanda suka taso a cikin irin wannan yanayi na rashin sanin uba ko ma uwa da uba kan fuskanci tsangwama da kyara daga al’umma

Matsayar musulunci kan nasabarsu

Sau da yawa, wadanda suka taso a cikin irin wannan yanayi na rashin sanin uba ko ma uwa da uba kan fuskanci tsangwama da kyara daga al’umma, har ma akan kira su da wasu sunaye da ke muzanta su.

Sai dai, a cewar Dakta Zahra’u wannan bai dace ba, kuma ba shi da asali a musulunci.

Image caption

Dakta Zahra’u ta ce bai dace a dinga tsangwamarsu ba don musulunci bai yarda da hakan ba

“Wallahi ba su da wani laifi don ba su ne suka yi zinar ba, iyayensu ne suka yi. Kuma ko su iyayen idan suka nemi gafara Ubangiji Mai Gafara ne da Jin Kai, zai dube su ya yafe musu. Don haka bai kamata al’umma su dinga kyamarsu tare da gudunsu ba,” kamar yadda ta ce.

Fatan yawancin wadannan yara dai shi ne al’umma ta gane hakan, a kuma daina tsangwamarsu, a kuma dauke su kamar sauran mutane.

[ad_2]

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...