Yadda matar talakan Najeriya ta fi matar gwamna morewa

[ad_1]

Babu shakka matar gwamna na daga cikin matan da dubban mata ke sha’awar rayuwar su kuma suke fatan ina ma su ma su kai wannan matsayi.

To sai dai watakila idan wasu matan suka ji yadda matan gwamnonin ke rayuwa za su ga cewa ba komai ba ne ya ke da dadi a rayuwarsu.

Kowane dan adam dai yana bukatar sirri a rayuwarsa, domin samun damar yin walwala yadda ya ke so.

A bangarensu, wasu matan gwamnoni na cewa ba su da wannan sirrin a rayuwar su.

Mai dakin gwamnan jihar Kebbi Hajiya Aisha Bagudu ta ce daya daga abuwan da ke damunta a matsayin matar gwamna shi ne rashin sirri.

Ta ce ko me ta ke yi ba ta da sirri, duk da cewa tana son shiga jama’a ba tare da ana yi mata wani kallon cewa wannan wata mata ce ta daban ba.

Wani kalubalen kuma a cewarta shi ne, yadda zama matar gwamna ya ke zame mata kalubale wajen tafi da kungiyarta.

Ta ce a da jama’a suna bawa kungiyar gudunmuwa, kuma duk kokarin da aka yi mutane suna yabawa.

Amma ta ce a yanzu mutane sun daina bai wa kungiyar gudunmuwa, kuma ba a yabawa da yunkurin da suka yi, sabo da ana ganin ta matar gwamna ce.

To amma Hajiya Aisha Bagudu ta ce kungiyar ta ba ta gwamnati ba ce, kuma ba da kudin gwamnati ta ke tafiyar da ita ba.

Kungiyar dai tana tallafawa rayuwar almajirai ne da mata marasa galihu.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...