Yadda mata ke neman mijin ‘rufin asiri’ ta intanet a Najeriya

Amarya

Duk wani namiji ko mace da ta kai wani munzali na manyance abu na farko da ake yi mata fata shi ne samun miji nagari.

Bisa al’adar Æ™asar Hausa namiji ne yake ganin mace idan hankalinsa ya kwanta da ita sai ya tura iyaye ko manyansa a nema masa izinin har a kai matakin soma batun aure.

Ko da yake a wasu lokutan akwai auren haɗi da iyaye kan yi wa ƴaƴansu don ƙarfafa zumunci ko abota tsakanin iyalai biyu.

Amma kamar yadda Hausawa ke cewa duniya juyi-juyi, kusan a wannan lokaci zamani ya zo da abubuwa da dama inda a wasu lokuta ma mace ke iya ganin namiji ta furta hankalinta ya natsu da shi ko tana fatan ya aure ta.

Wani abu kuma da ke sake jan hankali a wannan zamani shi ne yadda ake amfani da kafar sada zumunta ko intanet wajen neman miji ko mata.

Baya ga shafukan sada zumunta kamar Facebook da su Twitter da Instagram da wasu kan ce anan suka hadu, ana kuma samun shafukan da su aikinsu shine haÉ—in-aure da tallata bayanan mutum ga mabukacin ko a samu dacewa.

A kwanakin baya-bayanan a shafuka irinsu Northern Hisbiscus na Instagram kana iya iske bayanan mace da kuma irin namijin da take so, wasu kan ce mai kudi wasu kuma mai rufin asiri, ko wacce dai na bayyana irin abun da take so.

Haka zalika a Twitter akwai wani shafi mai sunan Halal Matchmaking, wanda suma ke wallafa bayanan mace ko namiji da sunan neman dacewa ga mai ra’ayi ko sha’awar aure.

Aisha Falke ita ce mai shafin Northern Hibiscus a Instagram da ke wallafa irin wannan bayanai na neman dacewa, a tattaunawarta da BBC Hausa ta bayyana hujjojin da suka sa mata ke neman miji ta shafukan sada zumunta a wannan zamani.

Ta ce duba da yanayi rayuwa da yadda abubuwa suka sauya gaskiya haduwa har ta kai ga an furta so na wahala.

“Galibi za ki ga mace ba ta wani fita ko zuwa wani wurin da za ta iya haduwa da namiji da zai furta yana sonta, akasari irin wadannan mata watakila daga makaranta sai gida ko wurin aiki, sannan ba wai motar haya ko dai wani yanayi za ta tsinci kanta ba, har ta kai ga an hadu, kuma karshenta ba ta da kawaye ma.”

Falke ta ce ganin sociyal midiya abu ne mai fadi, sai ki ga idan ta turo an yi dace, saboda akwai wanda in ba ta wannan hanya ba babu ta inda za a hadu.

Yaudara

Mata da dama na da fargaba, saboda akasarin mazan masu zuwa da yaudara sun fi yawa, wasu kawai zuwa suke da wata manufa su ci bilis su wuce kawai, don haka sukan bi wannan hanyar ne domin neman dacewa kuma gaskiya hakan na tasiri don mun sha haÉ—a aure.

To shin a kyauta ake wallafa bayanan neman mijin ko mata?

Mai shafin Nothern Hibiscus ta ce a rana suna samun sako É—aya zuwa biyu na matan da ke cewa a wallafa bayanansu da sunan neman miji, amma kuma duba da yadda abin ke da yawa shafin ba a kyauta yake amsa bukatar matan ba, ana cajin mutum da ke son a yi masa wannan talla naira dubu biyar.

Baya ga Northen hibiscus binciken da BBC ta yi ya nuna akwai irin wadannan shafuka da ke bayyana kansu a matsayin “Halal Matchmaking” a intanet, inda mata da maza ke shiga su yi rijista a caje su kudi don neman dacewa.

Bayanan da ke jikin shafin kafin yin rajista kashi-kashi ne, idan ka gamsu da sharuddansu sai ka yi rijista ka gwada sa’a ko ki gwada sa’arki.

Bayanan sauti
Hira Da Mai Dalilin Aure ta Kano

Son auren mai kudi

Falke ta ce akasari matan da ke zo mata na cewa ga irin mijin da suke so wasu ma masu kudi suke buƙata, kuma a cewarta suna yin haka ne domin samun kwanciyar hankali, aure babu rufin asiri gaskiya babu daɗi, wasu ma da ke cewa hakan ba wai lallai hamshaki suke so ba kawai dai ya kasance zai iya dauke mata matsalolinta.

Yaya hadin auren yake ƙarƙarewa?

Ta ce tun da ta soma wannan haÉ—i mutum guda take da tabbacin sun yi aure, ko da yake ta ce wasu daga an yi hadin ba ta sake jin É—uriyarsu, wasu kuma suna dawowa su ce ba su yi dace ba a sake tallata su.

Sharhi -Umaymah Sani Abdulmumin

Wannan bayanai na Falke ya nuna cewa alkunya da aka san mace da shi ya soma disashewa, la’akari da irin abubuwan da ke faruwa da watakil yaudara da fargabar halayen masu É“oye cewa ba da aure suka zo ba, sannan su É“ata wa mace lokaci ko su cika wandonsu da iska idan bukatar da ta kawo su ta cika.

Salon neman abokiya ko abokin zama don raya sunna ta intanet watakil ya kasance sabon abu ga wasu, amma idan za a iya tunawa tun fil’azal akwai abin da Bahaushe ke kira mai dalilin aure.

WaÉ—annan wasu rukunin mutane ne da dama aikinsu hadin-aure ta hanyar kai wa maza hotunan mata su zaba.

Don haka ganin irin wannan talla a shafukan intanet watakil sauyin zamani ne da sauki tun da yanzu an sake wayewa komai yana koma wa intanet.

Idan za a lura zumunci ma wahala yake, sannan hatta abokai ta wannan hanya ake haduwa har a ƙulla zumunci mai ƙarfi.

Sannan akwai matan aure da maza da ke ba da labarin sun yi dace ne ta irin wadanan shafukan sada zumunta na zamani.

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...