Yadda masallatan Makka da Madina suka kasance a ranar Juma’a – AREWA News

Tun bayan da aka samu rahoton yaɗuwar cutar Corona a wasu kasashen duniya, hukumomin kasar Saudiyya sun dauki matakan kariya domin hana cutar bazuwa.

A cikin matakan da suka fara dauka sun hada da dakatar da bayar da izinin zuwa aikin Umara ko kuma zuwa ziyara kasar.

Sai dai bayan da cutar ta zama annoba a fadin duniya hukumomin kasar suka dauki matakan ta kaita mutanen da suke shiga masallatan biyu.

Bayan da cutar ta fara bazuwa a kasar a yanzu dai an saka dokar hana fita baki daya a kasar a kokarin da hukumomin kasar suke na dakile bazuwar cutar

More from this stream

Recomended