Yadda coronavirus ta sauya bikin aure da na suna da makoki a Kenya

'Yan uwan Yassin Hussein na kuka kafin binne gawarsa a makabartar musulmai ta Kariokor dake Nairobi a Kenya ranar 13 ga watan Maris 2020.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu iyalai na zaman makokin mutuwar wani yaro dan shekara 13 da ‘yan sanda suka harbe bayan sanya dokar hana zirga-zirga

Daga jerin wasikunmu da muke samu daga ‘yan jarida a nahiyar Afrika, Joseph Warungu yayi duba kan yadda cutar ta sauya rayuwar ‘yan Kenya daga bikin suna zuwa na mutuwa.

Sheil Atieno na jiran kotakwana domin taimakawa wata mata dake da cikin da yakai mako 32 domin ta haihu. Dakta Atieno ta yi irin wannan taimako da yawa kafin wannan, amma ita wannan haihuwar zata zama ta daban ne shi ne dalili.

An kai mai cikin ne wani asibitin gwamnati dake Nairo babban birnin kasar, bayan an yi mata gwaji anga tana dauke da coronaviru.

Dakta Atieno, jami’ar tuntuba ce wajen tiyatar mata, da take cikin wata tawagar likitocin da aka amince su rika kula da matan da suka nuna alamun kamuwa da cutar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jami’an kiwon lafiya na cikin mummunan hadari kamuwa da coronavirus

Rayuwar Dakta Atieno ta sauya a hankali. Tana da yara biyu kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara biyu.

“Da matukar wuya yadda muke fama, musamman yadda nake lura da iyaye mata dake dauke da wannan cuta” kamar yadda ta shida mani.

“Ina daf da yin wata tiyatar fitar da jariri, wadda yawanci ke da alaka da fitar da ruwan jikin mata. Duk da cewa sai na sanya kayan kariya zan gudanar da tiyatar amma tana matukar tayar da hankali da kuma sanya dimuwa.

“Duk lokacin da naje gida, yarana basa son zuwa su rungumeni. Nima kuma ba zan iya taba su ba har sai na nayi wanka na kuma tsaftace kaina na sauya kaya.

“Abu ne mai matukar muya da tausayi. Amma ba ni da wani zabi da ya wuce hakan – aikina ne in karbi haihuwa ko da wannan annoba ko babu, in ji Dakta Atieno.”

Hakkin mallakar hoto
Francis Gitonga

Image caption

Francis da Veronica sun kwashe wata shida suna shirye-shiryen abin da za su kashe a aurensu

Sababbin Aure

Hakkin mallakar hoto
Francis Gitonga

Image caption

Francis da Veronica sun kwashe wata shida suna shirye-shiryen abin da za su kashe a aurensu

Francis da Veronica sabbin ma’aurata ne da ke cin amarcinsu a kauyensu na Nyahururu, wanda ke da tazarar kilomita 200 daga Nairobi.

Sun yi shirin a daura aurensu a ranar 5 ga watan Afrilu. Sun gayyaci mutane 500 domin su shaida wannan lokaci mai cike da tarihi a rayuwarsu, da su biyun za su ce: “Na yarda!”

Amma yayin auren mutane shida ne kawai aka amince su shiga cikin cocin domin shaida auren- amarya da ango, sai manyan abokansu biyu da kuma fasto biyu da za su daura auren. babu iyaye, babu yan uwa, babu abokansu na kauye.

Dokar nisantar juna da dokar takaita tafiye-tafiye da cutar Covid-19 ta janyo, ta hana daruruwan mutane halartar aurensu. Ma’auratan sun gudanar da walimar aurensu a gida da wasu mutum 12.

Suna da damar dage auren nasu har sai komai ya daidaita, amma suka zabi su yi yanzu.

Na tambayi ma’auratan ko sun yi nadama da ba su daga auren ba – ta yadda yan uwa da abokan arziki za su halarta.

“Aa babu wata nadama da muka yi,” in ji Gitonga, wanda ke aiki a cocin Redeemed Gospel dake Nyahururu.

“Mun ji kamar Ubangiji ne ya ce kawai a daura auren. Bayan haka kuma, Ni da Veronica muna son junanmu sosai, ba mu san junanmu ba kafin Ubangiji ya hada mu a coci.

Mista Gitona ta shaida min cewa Covid-19 ba kawai shirin aurensu ta sauya ba, ta kuma bijiro da wasu alfanu da ba su taba zatoba.

“A shirin da muka yi aurenmu zai lakume kimanin kudin Kenya shillings 300,000 kimanin dalar Amurka 2,800. Amma da baki ba su zo ba, ba kuma mukarbo hayar komi ba, a karshe Shillins 50,000 muka kashe.

“Yanzu kuma muna ta samun kira daga mutane daban-daban daga sassan Kenya, suna cewa mun basu karfin gwiwar yin nasu auren a wannan yanayin maimakon shirya babban aure wanda a karshe sai su kar da bashi a kansu.”

Auren wadannan mutanen ya zama babban labari a lokacin da ake tsaka da annobar coronaviru. Haka kuma ta sauya tsarin rayuwa a Kenya – ‘yar karamar soyayya – da ta dace da tsarin aljuhinmu mutane yayin yayin aure.

Zaman makokin da iyalan keyi

Yayin dokar ta baci da gwamnati ta kakaba a wani mataki na dakile yaduwar cutar, jami’an ‘yan sanda sun harbe Yassin Hussien Moyo.

Yassin ba shi kadai abin ya rutsa da shi ba. Mutane da yawa a fadin kasar na jinyar ‘yan uwansu da suka karye da wadanda suka ji munanan raunuka da dama saboda aikin jami’an ‘yan sanda na musamman da aka yi wa take da “Aiki don jin dadin kowa”.

Covid-19 ta bude wa gwamnati damar yin kama karya.

Mahaifin Yassin, Hussein Moyo, ya sosawa mutan kenya in da yake musu kaikayi yayin jana’izar dan nasa. ” da rana muna fama da tsoron cutar coronavirus da daddare kuma muna fama da kama karyar ‘yan sanda.”

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Yan uwa da abokan arziki na addu’a a gefen kabarin Yassin

Mafi yawan ‘yan Kenya dake samun kudi ba daga gwamnati ba, na korafin a gidajen radiyo da talabijin kan yadda suke fama da makiya uku – sabuwar cutar coronavirus, da yunwa da kuma ‘yan sanda.

Dan siyasar da aka tsangwama

James Orengo tsohon shahararren dan siyasa kuma zababben sanata ne daga babbar jam’iyyar adawa ta Orange Democratic Movement (ODM). Galibin yana yin abin da hankulan ‘yan kasar suka karkata a kai ne.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

James Orengo dan siyasa ne da yayi fice tare da wani lauya a tsaye

A wani zama na musamman na sauraren karar zabe a Junairun 2017, Mista Orengo wanda lauya ne, yayi magana kan hadari da ke tattare da zartar da dokoki mara sa kyau, kuma ya yiwa wakilan jam’iyya mai mulki jan kunnan kar su za sun saki jiki a gwamnati.

“A mafi yawan lokuta juyun juya hali na zama sanadin mutuwar ‘ya’yansu….. gwamnati ta hallaka mutanensu. Wannan gwamnati za ta hukunta ku sama da yadda zata hukunta ni, ina kuma shaida muku, nan da shekara mai zuwa za ku zo ofishi na kuna kuka kuna neman na wakilce ku.

Wannan bayanin mutan Kenya na matukar amfani da shi. Amma da zuwan Covid-19 bai fahimci yanayin da jama’a ke ciki ba lokacin da ya wallafa a shafinsa na Tiwita: ” Na tuka kaina zuwa majalisa domin amin gwajin Covid-19. Donmin bin ka’idar da aka shin fida don yaki da wannan annobar.

Martani mai zafi ya dawo cikin gaggawa.

“To ina ya ku bayi ake so su tuka kansu su je?” Tiwitan da wani dan Kenya yayi kenan, wani ma ya lkara da cewa: “Yan siyasa na zaton don sun tuka kansu sun yi wani babban abu ne. Meke damun wannan kasar ne?”

Overall, the Covid-19 crisis has wiped away politicians’ ubiquitous presence from the media and Kenyans seem to be enjoying the peace and quiet.

Akwai abubuwan da ba a maganar su a kafafen sadarwa saboda doka – hana ‘yan siyasa sa maganganu a labarai sai dai game da abin da ya shafi kiwon lafiya da makamantansu.

Dole ‘yan siyasa su damu kan mai zai faru in mutan Kenya suka saba rayuwa ba tare da su ba.

Dan gidan yarin dake da sa’a

Covis-19 ta tilastawa alkalai da kotunan majistiret a Kenya aiki da intanet domin gudanar da ayyukansu.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar hgakan wani mutum da ake zargin ya saci littafin injila a kantin zamani.

Bayan ci gaba da sauraron karar ta talabijin lokacin da ke karkashin kulawar yan sanda. Ya matukar jin dadin cewa yanzu za a ci gaba da sauraron karar tasa a matsayin mutum mai ‘yanci kuma alkalin yayi umarni a sake sa ba tare da biyan ko sisi ba.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Gwamnatoci a duniya na matukar nuna damuwa game da halin ‘yan kurkuku kan coronavirus

Yana daga cikin shirin gwamnatin na yaki da Covid-19 rage cunkoso a gidajen yari, wanda kuma tuni aka saki firsinoni 4,800 masu kananan laifi.

Babu mamaki mutumin da ake shari’arsa a kotu kan injila zai yi amfani da littafin ne domin addu’ar dakatar da yaduwar Covid-19 a fadin Kenya.

Akwai tabbacin rayuwa ba za ta dore a haka ba.

More from this stream

Recomended