Yadda aka mayar da Afirka saniyar ware a yakin Libya

Wani hoto da aka dauka a watan Nuwamban 2017, da ya nuna mayakan jagoran yan tawayen Libya Janar Khalifa Haftar

Yayin da manyan kasashen duniya ke cigaba da tsoma baki kan lamuran Libya, an mayar da kungiyar kawancen kasashen Afrika ta AU saniyar ware a kokarin da ake yi na warware ricikin da aka shafe shekaru ana fama dashi a kasar.

Alamun hakan sun bayyana ne a baya-bayan nan, yayin da manyan jami’an diplomasiyya ke gudanar da taruka a Berlin dake Jamus da kuma Moscow a Rasha don warware ricikin ba tare da sanya bakin kasashen Afrika ba.

Kasashen Afrikan dai na cigaba da kokawa game da yadda aka mayar da Libya tamkar wani dandalin gwada kwanji ko karfin makamai tsakanin manyan kasashen duniya masu karfin fada aji.

Ana ganin kamar yakin a yanzu ya zama na kasashen turai da Rasha da Turkiyya, ba tare da la’akari da cewa Libya kasa ce ta nahiyar Afrika ba, inji Jalel Harchaoui, wani mai sharhi kan harkokin Libya a cibiyar nazarin huldar kasashen duniya dake Holan.

Masu kutsen kasashen turai

Da yake bayyana damuwa game da lamarin, shugaban Uganda Yoweri Museveni ya fadawa BBC cewa sai da aka kusa kammala tarukan sannan aka gayyaci shugaban Congo Denis Sassou Nguesso zuwa taron warware rikicin na Libya da aka gudanar a Berlin dake Jamus.

“Kuskuren da muka yi shine na barin kasashen turawa su kutsa Libya a 2011, kamata yayi mu shiga lamarin ko da ta kama ayi gaba da gaba, ta yadda zasu gane kuskuren su”, inji shugaban na Uganda Yoweri Museveni.

”Idan Afrika taso fatattakar masu mamaya zamu iya yin hakan, mun fatattaki masu mamayar Portugal”, inji Museveni da yake wani shagube ga turawan Portugal da suka yiwa Afrika ta kudu mulkin mallaka har zuwa 1994.

To sai dai masu sharhi na cewa Afrikan ce ya kamata ta zargi kanta game da yadda aka kebance ta kan batun warware rikicin Libya.

Mr Nguessa dai ya taba jagorantar wani kwamitin kungiyar AU akan Libya, wanda ya gudanar da taruka daban-daban don warware rikicin kasar.

Ana mutunta Gaddafi a kungiyar AU saboda gudummawar makudan kudin da yake bata lokacin da yake raye, ya jima yana neman ganin kasashen Afrika sun hada kansu wuri guda domin kalubalantar duk wani yunkurin mamaya daga kasashen yammaci da kuma Amurika.

Menene abin da ya janyo rikicin Libya ?

Tutsun da aka yi masa ya aika wani babban sako ga yan Afrika, abin da ya janyo suka daga kasashe daban-daban.

Terek Megersi, wani mai fashin baki a cibiyar bincike kan harkokin kasashen turai dake Birtaniya. ya ce kalaman Museveni sun nuna cewa har yanzu wasu shugabannin Afrika basu dauki darasi daga abin da ya faru da tsohon shugaban Libya Muhammad Ghaddafi ba.

Yayin juyin juya halin na 2011 da aka yi a Libya, mutane da dama sun dauka cewa AU din na goyawa Ghaddafi baya, abinda ya janyo mata tsana daga wasu yan kasar ta Libya.

”A lokacin daruruwan miliyoyin daloli sun yi ta zagayawa saboda zuba jarin da gwamnatin Ghaddafi ta rika yi a kasashen Afrika, sai dai a yanzu abin ya canja”, in ji Mr Megarsi.

Ya kuma kara da cewa a yanzu wasu kasashen Afrika da dama na safarar yan cirani zuwa Libya.

Misali na baya-bayan nan shine wani rahoto da ya bayyana cewa ana yaudarar wasu yan Sudan da sunan basu aikin tsaro a hadaddiyar daular Larabawa, amma sai a bige da ajiye su gadin cibiyoyin man fetur da jagoran yan tawayen Libya Janar Khalifa Haftar ya kwace.

Libya na da rumbun ajiyar man fetur mafi girma a Afrika, baya ga arzikin iskar Gas da ubangiji ya huwace mata, abin da ya janyo masu sha’awar zuba jari daga kasashe daban-daban na duniya.

Sai dai yakin ya janyo wa kasar gagarumar asara saboda an rufe cibiyoyin mai da yawa saboda farmakin jagoran yan tawayen kasar Khalifa Haftar.

Su wanene ke da hannu kan lamarin dake faruwa a Libya ?

Hadaddiyar daular larabawa da Faransa ne manyan masu marawa Haftar baya a aniyar sa ta karbe iko da birnin Tripoli don zaman shugaban kasa.

Wata kasar kuma dake mara masa baya ita ce Masar.

Faransa kauwa na ganin cewa lokaci bai yi ba da Libya zata koma kan tafarkin dimukradiyya ka’in da na’in, sannan bata da ra’ayin masu kishin addinin musulunci su karbi kasar don gudun yi mata tutsu.

President Putin and President Macron

Masar wacce ke kallon kanta a matsayin mafi kusanci da kasashen larabawa maimakon na Afrika, na marawa Haftar da mayakan sa baya, amma abin bai zo da mamaki ba, saboda tana kokarin yaki da kafa gwamantin yan uwa musulmi tun lokacin da shugaban kasar Abdulfatah Alsisi ya yi juyin mulki a 2013 bayan kifar da gwamnatin yan uwa musulmi ta Muhammad Morsi.

Tana mara wa Haftar baya a siyasance, sai dai kwandalar ta bata ciwon kai da sunan taimaka masa.

Ana kallon sojojin Chadi a matsayin kwararrun mayaka

Wacce rawa Chadi ke takawa ?

A kashin gaskiya, kamata yayi shugaban Chadi Idris Deby ya goyawa Haftar baya, sai dai babu jituwa a tsakanin su.

Dalili kuwa shine Haftar na daga cikin sojin Ghaddafi da suka yiwa Chadi kutse a 1980.

Tun daga wannan lokacin aka rika samun tsama a tsakanin su.

Kamar Mali, da Niger da Burkina Faso, Chadi na da ra’ayin cewa akwai bukatar samar da kakkarfar rundunar soji a kudu maso yammacin Libya don kare kansu daga hare-haren bangarorin dake rikici da juna a Libya.

Har zuwa 2018, yan ta’adda na amfani da wannan wuri don sake shiri da kuma harkallar makamai, inji wani masani da ake kira Harchaou .

Toh sai dai ta’addanci a Sahel na cigaba da samun gindin zama, matasan da basu da aikin yi na cigaba da shiga aiyukan ta’addanci.

Darasin da ya kamata kasashen Afrika su dauka daga rikicin Libya

A cewar Mr Mergesi, tasirin kasashen Afrika a Libya ya ragu ne sabo da manyan kasasehen nahiyar kamar su Afrika ta kudu sun kasance a matsayin magoya bayan kasashen da suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muhammad Ghaddafi.

Ya kuma kara da cewa kasashe da dama sun karbe kadarorin Libya kamar su otal-otal a maimakon maida su ga hukumomin kasar.

Wannan ya janyowa kasashen Afrika da dama bakin jini a idon yan kasar ta Libya, ko da yake zasu iya taimakawa don kawo karshen rikicin kasar.

Afrika bata taka rawar da ya kamata ace tana takawa a Libya, kasashe irin su Afrika ta kudu da Sierra Leone sun warware rikice-rikicen su ta hanyar sasantawa, don haka zasu iya taimakawa Libya don warware na ta matsalolin, in ji Mergesi.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...