Yadda aka kashe yan sanda 6 cikin sa’o’i 24

Cikin kasa da sa’o’i 24 yan sanda shida aka kashe a hare-hare daban-daban da aka kai musu a jihohin Rivers da Bayelsa.

A ranar Litinin wasu yan sanda biyu dake rakiyar motar daukar kudi wasu yan bindiga da ba’a san ko suwaye ba suka harbe su har lahira a Fatakawal babban birnin jihar.

Rahotonni sun bayyana cewa an kai wa ya sandan hari ne a wani shingen bincike dake yankin Ojoto a babban birnin jihar.

Yan bindigar sun debe bindigogin ya sandan da suka mutu da kuma wasu kudade da ba a bayyana yawansu ba.

Nnamdi Omoni mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce tuni rundunar ta kama mutane 9 da ake zargin suna da hannu a lamarin.

Sa’o’i kaɗan bayan harin na Rivers wasu yan bindigar na daban sun farma ofishin yansanda dake Agudama a jihar Bayelsa inda suka kashe yan sanda hudu ciki har da wata yar sanda dake dauke da juna biyu.

Wasu majiyoyi dake yankin sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da bindigogi da harsashi a harin da suka kaddamar da misalin karfe 2 na dare.

More from this stream

Recomended