Yadda ƴansanda suka taimakawa wani mai mota

[ad_1]








Duk da irin kallon da wasu suke wa jami’an ƴansanda na rashin tabuka komai da kuma yadda wasunsu suka kware wajen karbar na goro da kirkiro laifi a ɗorawa mutum bai jaba bai gani ba.

Sai dai ba dukkanin jami’an ƴansanda bane suke da irin wadancan halaye akwai wadanda kirkinsu da kuma yin aiki bisa ka’ida shi kaɗai suka sanya a gaba.

Irin waɗannan ƴansanda ne suka taimakawa wani mutum ya sauya tayar motarsa lokacin da ta yi faci akan babbar gadar nan ta Third Mainland A jihar Lagos.

Bayan sun kammala taimakon nasa jami’an sun juya sun tafi ba tare da sun nemi wani abu daga wurin saba abinda ba kasafai ya fiya faruwa ba a tsakanin jami’an ƴansanda.

A karshe mutumin ya godewa ƴansandan tare da jinjina musu kan wannan hali na kwarai da suka nuna.




[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...