Ƴan sanda a jihar Kano sun ɗakile wani yunkuri da wasu ɓatagari suka yi na kai hari gidan Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyar APC na jihar Kano.
A wata sanarwa ranar Lahadi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce rundunar ta karɓi kiran kai ɗaukin gaggawa da misalin ƙarfe 06:30 na yamma daga kwanar unguwar Chiranchi dake ƙaramar hukumar Gwale.
Kiyawa ya ce ɓata garin sun riƙa jifan mutane da duwatsu a ƙoƙarin da suka yi na shiga gidan shugaban jam’iyar.
“Tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin DPOn ƴan sanda na Gwale su ne suka kai ɗauki suka daƙile yunkurin shiga gidan inda suka dawo da zaman lafiya a unguwar,” a cewar sanarwar.
Kiyawa ya ce ba a kama kowa ba kan rikicin amma bincike ya nuna cewa lamarin da ya faru rikici ne tsakanin wasu ƴan daba.
“Waɗanda suka haddasa rikicin sun haɗa da AbdulYassar, da aka fi sani da Jonny, Birbiri, da kuma Jinjiri Aljan,” ya ce.
Kiyawa ya ce ana cigaba da ƙoƙarin ganin kamo su.