Ya kamata United ta fara da Ronaldo a wasan Everton – Sir Ferguson

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
ronaldo ya ci kwallo biyar a wasa takwas da ya buga wa Manchester United a bana

Sir Alex Ferguson ya ce ya kamata a ce Manchester United ta fara da Cristiano Ronaldo a gasar Premier League da ta kara da Everton.

Ranar Asabar United ta karbi bakuncin Everton a wasan mako na bakwai a babbar gasar Ingila da suka tashi 1-1 a Old Trafford.

Ole Gunnar Solskjaer bai fara wasan da Ronaldo da kuma Paul Pogba ba da suka yi zaman benci, sai da aka koma zagaye na biyu ya saka su a fafatawar.

Ronaldo ya shiga karawar lokacin da United ke cin kwallo daya, daga baya Everton ta farke da ta kai suka tashi 1-1 a wasan.

Kawo yanzu Ronaldo ya ci kwallo biyar a wasa takwas da ya buga wa United wadda ya koma a bana daga Juventus.

Kyaftin din tawagar Portugal ya fada cewar Sir Ferguson ya taka rawar gani da ya amince ya sake komawa Old Trafford a karo na biyu.

United ta hada maki 14 a wasa bakwai a Premier League, za kuma ta fafata a wasan gaba da Leicester City ranar 16 ga watan Oktoba.

More from this stream

Recomended