Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a faɗin ƙasa baki ɗaya.

Sarkin ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis bayan ganawar da sarakunan gargajiya suka yi da shugaban ƙasa, Bola Tinubu a fadar Aso Rock dake Abuja.

Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba Najeriya za ta dawo matsayinta na uwa maba da mama a nahiyar Afirka.

“Shugaban ƙasa ya bamu jadawalin tsare-tsaren abubuwan da yake ta yi kuma muna fatan da izinin Allah abubuwa za su dawo dai-dai,” ya ce.

“Babu mutumin da ba zai damu ba akan zanga-zanga a ko’ina ne a duniya munga abun da ya faru a wasu ƙasashe inda aka kayar da gwamnati.”

Mai martaba sarkin ya ce saboda haka ne suke kira da mutane da su amsa kiran da ake yi musu na suyi hakuri su bawa gwamnati lokaci.

More from this stream

Recomended