Alamu na nuni da cewa wutar rikicin da ta kunno kai a jam’iyar APC na neman zama gobara daga kogi maganinki sai Allah.
Biyo bayan sauke shugaban kwamitin riko na jam’iyar, Mai Mala Buni daga kan mukaminsa aka kuma maye gurbinsa da gwamnan jihar Niger, Abubakar Sani Bello.
Kwana guda bayan faruwar haka sai gashi sakataren riko na jam’iyar, John James Akpanudoedehe ya sanar da ajiye mukaminsa.
Sakataren ya mika takardar murabus nasa ga sabon shugaban rikon jam’iyar.