Wuta ta kama tashar jirgin ƙasa na zamani a Legas

Wuta ta tashi a kan wani ƙaramin yanki na layin Lagos Blue Line a wuri da ke fuskantar tashar NEPA, kusa da gadar Eko, a yankin Apogbon na Jihar Lagos.

A cewar wani rubutu da Gboyega Akosile, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya wallafa a shafin sa na X.com @gboyegakosile, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:12 na yamma ranar Asabar.

Akosile ya kuma bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, sannan babu wani jirgin ƙasa da ke aiki a lokacin da abin ya faru.

Ya ƙara da cewa tawagar ƙwararrun ma’aikatan lafiya da masu aikin ceto, tare da sauran masu amsa kira na farko, sun kashe wutar gaba ɗaya.

Related Articles