Wata wuta mai muni ta yi kaca-kaca da kasuwa guda ɗaya tilo da ke Trademore Estate, Lugbe, Abuja, da sanyin safiyar Litinin, lamarin da ya bar mazauna unguwar cikin alhini.
Wutar, wadda rahotanni suka ce ta fara ci kusan ƙarfe 3:30 na safe bayan da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya dawo da wuta, ta yi ƙamari kafin ma’aikatan ceto su samu damar kai ɗauki, a cewar rahotanni.
Duk da cewa ba a tantance ainihin musabbabin wutar ba, wasu shaidu sun yi zargin cewa matsalar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.
Wani mazaunin unguwar mai suna Joe, wanda ya fara gano wutar, ya bayyana wa manema labarai cewa lamarin ya firgita mutane.
“An sanar da ni kusan ƙarfe 4:00 na safe, kuma a lokacin wutar ta riga ta game dukkan kasuwar. Ba za mu iya tabbatar da ainihin musabbabin wutar nan take ba, amma muna zaton matsalar wutar lantarki ce,” in ji Joe.
Duk kokarin da mazauna suka yi na tuntuɓar Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Babban Birnin Tarayya bai sami nasara nan take ba.
Sai dai Joe ya ce ma’aikatan kashe gobara na Dunamis Church sun iso wurin kusan ƙarfe 5:00 na safe, sannan suka biyo bayan su ma’aikatan kashe gobara na Hukumar EFCC da na Sauka Station.