Wole Soyinka da Buhari na musayar yawu kan kama Sowore

Wole Soyinka
Image caption

Wole Soyinka ya yi fice wurin sukar gwamnatocin Najeriya daban daban

Fitaccen marubucin nan da ya lashe kyautar Nobel ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na kama daya daga cikin ‘yan hamayyar kasar, Omoyele Sowore bisa zargin shirya gangamin kawo sauyi da aka yi wa lakabi da RevolutionNow.

Wole Soyinka ya kamanta matakin da gwamnatin ta dauka da cewa ya yi kama da irin abubuwan da suka rinka faruwa a lokacin mulkin “kama-karya na marigayi Janar Sani Abacha”.

Sai dai mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Mista Soyinka da sauran masu korafi kan matakin da gwamnatin ta dauka suna son bata mata suna ne kawai, domin ba zai yiwu ta zuba ido ta bar mutane su dauki doka a hannunsu ba.

A karshen mako ne jami’an tsaron farin kaya na DSS suka yi dirar mikiya a gidan tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC kuma mamallakin kafar yada labarai ta Sahara Reporters a Legas, inda suka yi awon-gaba da shi, lamarin da ya janyo suka daga bangarori da dama.

Sowore tare da kungiyar Coalition for Revolution sun yi kira ga ‘yan kasar ne da su fito kan tituna domin yin zanga-zanga daga ranar Litinin domin kwatar ‘yancinsu da kuma kawar da abin da suka kira gwamnatin da ta gaza ta kowacce fuska.

Farfesa Soyinka ya fada a wata sanarwa cewar “Mun fuskanci irin wannan yanayi karkashin mulkin Sani Abacha lokacin da ya tura wasu dakaru na musamman domin tarwatsa wani shirin zanga-zanga ta kasa a makarantar Tai Solarin School, Ikenne”.

Baya ga Soyinka, kungiyoyin kare hakkin bil’adama irin su SERAP da Atiku Abubakar duk sun soki matakin na kama Sowore, wanda ya yi fice wurin sukar dukkan shugabannin siyasar da aka yi a kasar na baya-bayan nan.

Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawuyn Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya fitar ta ce masu wadannan maganganu ba sa yi wa gwamnati adalci kuma suna neman bata mata suna ne kawai.

Muna ganin kimar wasu daga cikin masu wadannan kalaman. Idan aka samu matsala ta tsaro suna cewa ‘yan sanda ba sa yin abin da ya kamata, “tare da neman a hukunta masu laifi ba tare da kakkautawa ba”.

“Amma yanzu ga shi an samu shugaban ‘yan sanda da ya ta shi tsaye domin ganin cewa ba a yi wa doka karan-tsaye ba amma suna cewa ka da a dauki mataki.”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaba Muhammadu Buhari ya musanta cewa yana mulkin kama-karya

“Wannan batun da suke yi na kwatanta Shugaba Buhari da masu mulkin kama-karya ba zai hana ‘yan sanda yin aikinsu ba,” a cewar Malam Garba.

Tuni dai kawunan ‘yan kasar ya rabu kan kiraye-kirayen zanga-zangar da kuma batun kame daya daga cikin jagororin da ke shirya ta.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta gargadi jama’a ka da su fito zanga-zangar, ta na mai cewa yin hakan “ta’addanci ne”.

Abin jira a gani shi ne ko masu zanga-zangar za su fito kamar yadda suka yi alkawari, ko kuma za ta kare ne a kafafen sada zumunta.

Batun kama Sowore na tashe a Soshiyal Midiya

Batun kame Sowore da DSS suka ya zama babban batu a shafukan sada zumunta musamman Twitter. Tuni mutane suka kirkiri wani maudu’i na neman a saki dan jaridar wato ‘#FreeSowore’.

Wannan na cewa ‘yan Najeriya na neman a saki Sowore. Zanga-zanga ai ba garkuwa da mutane ba ne.

Shi kuma wannan yana fadin cewa yin zanga-zanga ‘yancin dan adam ne a duk duniya saboda haka suke neman Shugaba Buhari ‘ya saki’ Sowore ba tare da bata lokaci ba.

Sai wannan da yake gama Shugaba Buhari da Allah da ya ‘saki’ Sowore.

#RevolutionNow

A farkon makon da ya gabata ne dai mai kamfanin jaridar ta Sahara Reporters ya fito da maudu’i a kafafen sada zumunta na #RevolutionNow domin yin zanga-zangar matsa wa gwamnatin Muhammadu Buhari lamba ta gyara zamanta.

Rahotanni sun ce wasu kungiyoyi masu fafutukar yaki da rashawa da cin hanci da kuma na kare hakkin dan adam kamar Amnesty International sun ‘kwarara wa’ masu son yin juyin juya-halin guiwa.

Hakan ne ya sa a ranar Alhamis fadar shugaban Najeriya ta fito da wata sanarwa inda ta ce duk abin da ya faru a kasar to ta dora alhakin hakan kan kungiyar Amnesty International.

A ranar Juma’a kuma an samu gomman ‘yan Najeriya da suka yi dandazo a kofar ofishin kungiyar ta Amnesty da ke Abuja domin yin zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu da ‘goyon bayan’ da aka ce kungiyar ta bai wa masu son yin juyin juya-halin.

Hakkin mallakar hoto
Sahara Reporters

Image caption

Omoyele Sowore ne ya kirkiro maudu’in ‘RevolutionNow’

To sai dai kungiyar Amnesty International a wata sanarwa da ta aike wa da BBC ta ce “aikinta shi ne sa ido kan tabbatar da kare hakkokin bil’adama ba siyasa ba.”

Sanarwar ta kara da cewa “tun 1967 Amnesty International take aiki – na tunatar da gwamnatoci kan kare hakkin dan adam da kuma tabbatar da cewa duk wanda aka zalunta an bi masa hakkinsa.”

“Saboda haka, kungiyar Amnesty za ta ci gaba da kira ga gwamnatin Najeriya wajen ganin ta gudanar da bincike kan zarge-zargen cin zarafin bil’adama da suka hada da fyade, azabtarwa, tsarewa da kisan mutane ba bisa ka’ida ba.” In ji sanarwar

Daga karshe Amnesty ta ce “Duk da mutanen da gwamnati take biya su yi wa kungiyar zanga-zanga, to ba za mu yi shiru ba. Kuma za mu ci gaba da bankado rashin adalci da cin zarafi da nuna wa mata banbanci da duk wani nau’in danne wa ‘yan Najeriya hakkokinsu a duk inda muka ga ana yi.”

More from this stream

Recomended