
Wata mota dake tafiya akan titi ta ƙwace inda ta shiga cikin jerin gwanon al’ummar Kiristoci dake kan hanyarsu ta zuwa gidan gwamnati da kuma fadar Sarkin Gombe domin gaisuwar bikin Kirsimeti.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na rana a kusa da wajen sanannen gidan abincin nan wato IMAN dake kan titin zuwa Bauchi.
Ana dai zargin cewa birki ne ya kwacewa motar tayi cikin mutane abun da ya haifar musu da fargaba tare da jikkata mutane da dama.
Faruwar lamarin ta harzuƙa mutanen har ta kai sun nemi su jikkata direban amma ya tsere kana daga bisani suka ƙona motar da kuma kayan dake ciki.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibitin koyarwa na tarayya dake Gombe.