Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi nasarar damƙe wata mata mai suna Rahama Sulaiman da zargin yin garkuwa da ƴar da ta haifa.
Rahotannin da muka sun nuna cewa Rahama dai tana neman kuɗin fansa har naira miliyan uku.
A cewar ƴan sandan, sun samu rahoto daga mijin matar, Kabiru Shehu Sharaɗa, kan cewa, Rahama Sulaiman mai shekaru 25, ta sanar da shi ƴarsa Hafsat Kabiru mai shekaru 6 ta ɓata ba a gan ta ba.
Bayan gudanar da bincike sai aka gano cewa Rahama Sulaiman ta ɓoye yarinyar ne, a Madobi, domin yin amfani da wannan damar don neman kuɗin fansa.
Ƴan sanda sun kamo ta, domin ci gaba da bincike, sai dai rahotanni na nuni da cewa, mijin matar ya mayar da ita gidansa tun a wajen ‘yan sandan, bayan sakin da ya yi.