Wata Mata Ta Nemi Kotu Da Ta Raba Aurenta Da Mijinta Domin Yana Takura Mata Da Jima’i

[ad_1]
A ranar Laraba ne kotun dake Iseyin jihar Oyo ta warware auren Baliki Oke da mijinta Arowolo bayan kuka da ta kai cewa yana matsa mata da yawan jima’I.

” Shekarun mu 7 da aure amma kuma abin sai kara gaba yake. Kullum dai aka hadu ayi harka. Ya kan dawo daga office da rana tsaka don ya kwanta dani, bayan haka ya koma wurin aiki, Hakan bai hana shi nema na da dare kullum ne kuma.”

Baliki ta ce mijinta kan lakada mata duka a duk ranar da ta ki amince masa domin shi a ra’ayinsa sai ya kwana da mace sau bakwai a rana sannan yake gamsuwa.

Gogan naka kuwa bai musanta haka ba, Arowolo yace tabas yawan son kwana da mace ya zama masa matsala a rayuwa domin har ya nemi magani kan haka.

Arowolo ya roki kotu da kada ta raba auren su cewa ya yi alkawarin neman taimako akan matsalar da yake fama da shi.

Alkalin kotun Adelodun Raheem ya raba auren Baliki da Arowolo kan cewa Baliki da ‘yan uwan ta sun dage cewa ba za ta ci gaba da auren ba.
[ad_2]

More News

Wani mahajjacin Jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya a Makka

Allah ya yi wa wani mahajjacin jihar Filato Ismaila Musa rasuwa a birnin Makka na kasar Saudiyya.Daiyabu Dauda, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai...

NAFDAC ta ce kar ƴan Najeriya su riƙa cin abincin da ya wuce kwana 3 a firij

Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a cikin firiji sama da kwanaki...

Ƴanbindiga sun kashe mutane a Jihar Kaduna

An tabbatar da mutuwar mutane shida yayin da wasu da dama tare da yin garkuwa da su a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka...

Obasanjo ya kai wa Remi Tinubu ziyara

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga, Oluremi Tinubu mai ɗakin shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu . Obasanjo ya ziyarci matar shugaban ƙasar a...